✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dan Atiku ya kamu da COVID-19

An samu daya daga cikin ‘ya’yan tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Atiku Abubakar da cutar COVID-19. Atiku, wanda shi ne dan takarar shugabancin kasa na jam’iyyar…

An samu daya daga cikin ‘ya’yan tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Atiku Abubakar da cutar COVID-19.
Atiku, wanda shi ne dan takarar shugabancin kasa na jam’iyyar PDP a zaben 2019, ya bayyana hakan ne a shafinsa na Twitter.
“An sanar da Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa (NCDC) kamar yadda doka ta tanada, kuma an kai shi Asibitin Koyarwa na Jami’ar Abuja da ke Gwagwalada don a yi jinyarsa”, inji Atiku.
Sai dai tsohon Mataimakin Shugaban Kasar bai fadi sunan dan nashi da ya kamu ba kuma bai yi bayani ba a kan ko ta hanyar mu’amala da mai dauke da cutar ya kamu ko dawowa ya yi daga kasar waje.
Zuwa yanzu dai hukumar ta NCDC ba ta tabbatar da samun wannan bayani ba.
A makon jiya uwargidan Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ta wallafa cewa ”yarta ta killace kanta bayan ta dawo daga Birtaniya.