✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dalilin tsadar siminti a Najeriya — Dangote

Farashin siminti a Najeriya ya fi na kasar Ghana da Zambia rahusa.

Kamfanin siminti na Dangote, ya ce farashin buhun siminti daya tun daga masana’anta ta Obajana yana fitowa ne a kan Naira 2,450 yayin da kuma na masana’antar Ibese yake fitowa  a kan Naira 2,510.

Babban Daraktan tsare-tsare na kamfanin, Mista Devakumar Edwin ne ya bayyana hakan yayin zanta wa da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ranar Talata a Lokoja, babban birnin Jihar Kogi.

Ya ce wannan farashi da suke sayar da simintin ya kunshi har da harajin da gwamnati ta sanya a kan kayayyaki.

A cewarsa, wannan karin haske na zuwa ne a daidai lokacin da ake rade-radin cewa kamfanin na sayar da siminti kan farashi mai tsada a Najeriya fiye da yadda ake sayar wa a wasu kasashen musamman Ghana da Zambia.

“A yayin da muke sayar da duk buhun siminti a kan farashi kwatankwacin $5.1 a Najeriya, ana sayar da shi a kan $7.2 a Ghana da kuma $5.95 a Zambia, wanda ya hada da dukkan haraji” in ji Edwin.

A cewarsa, duk da cewa kamfanin yana da iko a kan farashin fitowar buhun siminti daga masana’anta, sai dai ba su da iko a kan farashinsa da zarar ya shiga kasuwa.

Mista Edwin ya bayyana rashin jin dadinsa kan yadda wasu ke neman bata sunan Kamfanin Dangote da gangan, wadanda ke cewa yana sayar da siminti kan farashi mai tsada a Najeriya fiye da wasu kasashen Afirka.

“Wannan zargi ba wani abu bane face yaudara wacce ba ta da tushe ballanta asali,” in ji shi.

Ya alakanta tsadar siminti a Najeriya da karuwar bukatarsa a kasuwar duniya sakamakon illar da annobar Coronavirus ta haifar.