✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dalilin da ya sa jami’o’i masu zaman kansu ke neman a bude makarantu –ASUU

Kasuwarsu ta daina garawa shi ya sa suka matsa a ci gaba da harkokin karatu a jami’o’i

Kungiyar Malaman Jami’o’in Najeriya ASUU, ta sanar cewa jami’o’i masu zaman kansu wanda a halin yanzu kasuwarsu ta daina garawa su ne ke faman kiraye-kirayen a dawo da ci gaba da harkokin karatu a jami’o’in kasar.

Shugaban Kungiyar ASUU reshen jihar Kano, Kwamaret Abdulkadir Muhammad, shi ne ya sanar da hakan yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a Jami’ar Bayero da ke birnin Kano.

Kwamaret Abdulkadir ya ce wadannan jami’o’i su ne masu hura wutar a dawo da harkokin karatu sakamakon tsaikon da annobar coronavirus ta haifar a harkokinsu na samu.

Sai dai ya ce jami’o’in sun kulla wannan aniya ba tare da la’akari da tasirin da za ta yi ga lafiyar al’umma ba.

Yana cewa: “A hakikanin gaskiya, jami’o’in Najeriya ba su da ikon tanada da kuma kiyaye dukkanin sharudan da mahukuntan lafiya suka gindaya ba na dakile yaduwar cutar coronavirus kafin a iya bude makarantu ba.

“Mafi akasarin ‘yan kungiyarmu sun kai matakin Farfesa wanda kuma galibi dattawa ne da shekarunsu na cikin rukunin wadanda suka fi hadarin kamuwa da cutar.

“Saboda haka a yanzu babu wani shiri da muka sa gaba face bai wa lafiyarsu da ta dalibai muhimmanci”, inji shi.

Da wannan yake cewa, bai kamata gwamnati ta mika wuya ga wannan matsin lambar ba domin kuwa kungiyar ASUU za ta dora alhaki a kan Gwamnatin Tarayya yayin da duk wani abu ya faru ga ‘ya’yanta a wannan lokaci da likafar annobar COVID 19 ke ci gaba.

Yayin jaddada muhimmancin lafiyar mambobinta da daliba, ya kuma sanar cewa ASUU ba ta kyamar bude jami’o’in a yanzu amma kafin yin hakan dole ne a tanadi dukkan matakan da suka dace.