✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dalilin da na rubuta wa Buhari wasika —Turji

Turji ya ce tausayin talakawa da ake kashewa ya sa shi rubuta wasikar neman sulhu

Fitaccen dan bindigar nan da ya addabi wasu yankunan Arewa maso Yammacin Najeriya, Bello Turji, ya ce tausayin talakawa da jami’an tsaro suke kashewa ne ya sa shi rubuta wa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari wasikar neman sulhu.

Turji ya bayyana cewa akwai wasu mayanka biyu da ake yanka mutane a yankin da yake, kuma ’yan uwansa ake yankawa a irin wadanna mahauta akalla guda biyu.

A hirar da Aminiya ta yi da shi a maboyarsa, Turji ya bayyana cewa, “A Najeriya, kuma gwamanti ba ta san da wannan kwata ba, amma ni na san da ita saboda ’yan uwana ake yankawa, maza da mata, a wurin.”

Ya zargi gwamnati da yaudarar ’yan bindiga, tana sa jami’an tsaro su kashe su, bayan ta sa sun lallashi juna sun mika mata makamansu da sunan zaman lafiya.

“Mun fara daukar ’yan uwanmu suna ba da makamai, ana zaunawa lafiya, [amma] kuma gwamnatin daga baya ta juya mana baya, ta sa suka yi ta kashe mu,” inji Turji, wanda ya fitini jihohin Zamfara da Sakkwato da makwabtansu.

‘Muna son sulhu’

Amma a cewarsa, duk da haka, suna jiran ganin matakin da gwamnati za ta dauka, duk da cewa alkawuran da ta yi musu amma ta karya, “Ai ba su kirgiwa, idan na fara kirga maka su yanzu sai ka ce innalillahi.”

Ya ce idan gwamnati ta yi sulhu da su, a shirye suke su cika alkawarin da suka dauka, idan har ita ma ta cika nata bangaren alkawarin.

“Idan gwamnati ta cika alkawari, mu da ma ba wata kungiya muke so mu kafa ta addini ba, ba wata kungiya muke so mu kafa ta wata kasa ta kanmu ba, ba wata kungiya ta siyasa muke nema ba. Mu saboda rayukan ’yan uwanmu ne kawai muka dauki bindiga,” inji shi.

Dan bindigar ya bayyana cewa abin da suke so daga gwamnati shi ne ta dauki mataki a kan ’yan sa-kai, wadanda yake zargi da cin zalin Fulani da kuma yi musu kisan gilla.