✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dalilin da na ki halartar taron titsiye a Kaduna —Kwankwaso

Tarko aka kafa min a Kaduna

Dan takarar Shugaban Kasar a karkashin Jam’iyyar NNPP, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya bayyana dalillinsa na kaurace wa taron titsiye da Kungiyar Dattawan Arewa ta shirya ga ’yan takarar Shugaban Kasa a Jihar Kaduna.

Tsohon Gwamnan na Jihar Kano ya ce ya yi haka ne saboda gudun kada a nemi su janye wa wani daga cikinsu.

‘Tarko aka kafa min a Kaduna’

Kwankwaso ya yi karin haske kan dalilin da ya sa ya ki amsa gayyatar kungiyoyin Arewa domin bayyana kudirorinsa ga yankin Arewa.

A cewar a “Shi ya sa aka kafa tarko a Kaduna, suna so idan na je na yi bayani, daga baya su ce ga wani dan takara shi ya fi cancanta.”

’Yan takarar Shugaban Kasa hudu ne suka halarci tattaunawar da gamayyar kungiyoyi masu kare muradun Arewa suka shirya.

Kungiyoyin da suka shirya taron sun ce manufarsu ita ce su ji bayanai daga ’yan takara kan tanadin da suka yi wa yankin, sannan su fada wa dan takarar nasu bukatun.

Haka kuma Kwankwaso ya bayyana jam’iyyun PDP da APC a matsayin matattun jam’iyyu wadanda wa’adi kadan ya rage musu su shiga kabari.

“Duk wadannan jam’iyyu sun rube. Duk wanda ya ce da kai PDP jam’iyya ce ko APC jam’iyya ce, to bai san abin da yake yi ba. Idan kuma yana shakka ya zo mu yi magana da shi.”

“Duk wadanda suke cikin PDP babu wanda zai gaya min PDP. Haka babu wanda ke cikin APC da zai gaya min APC,” in ji shi.

Ya bayyana cewa, ya fita daga jam’iyyun biyu ne saboda manufarsu ta saba da kare muradun talakawa.

Ya ce, “Na ga cewa ba wurin zama ba ne. Akidarsu ba mai kyau ba ce, niyyarsu da aikinsu ba masu kyau ba ne.

“Shi ya sa muka samu kanmu a halin da muke ciki yanzu.

Wadanan mutane Allah ya toshe basirarsu. Shi ya sa suka bari na fita daga cikinsu ga shi nan suna cizon yatsa.”

Ya ce, idan ba a samar da canjin jam’iyyun nan a matakan shugabanci ba, to babu shakka kasar nan za ta shiga cikin wani hali da ba a taba tsammani ba.

“Idan har ba a canza wadannan jam’iyyu ba to ina tabbatar maka sai an shiga matsalar da kowa ba ya zato domin takwas a tara da 16 daidai take da matsalar da muke ciki a Najeriya,” in ji shi.

Ya kuma musanta abin da ake yi cewa Jam’iyyar NNPP iyakacinta Arewa inda ya ce “To ai wurina hakan babu laifi.

“Wani ma cewa yake yi wai Kano ne da ni, wani kuma ya ce Arewa maso Yamma kadai. Duk abin da mutane suke fadi muna ji.

“’Yan Najeriya kuma suna jin su suna kallon su. Ai da ganin yadda wadancan jam’iyyu suke tafiya kowa ya san tamu ba irin tasu ba ce.

“Mu za mu fito da tsarinmu wanda zai zama karbabe a wurin jama’a.”

Sanata Kwankwaso ya kuma musanta hasashen da ’yan siyasa ke yi cewa a karshe zai iya janye wa wata jam’iyya daga cikin manyan jam’iyyun a zaben 2023, inda ya ce “Wadanne jam’iyyu? Rubababun? Akan me zan janye musu?

“Babu wanda zan janye wa. Zaben da za a yi a 2023 zabe ne tsakanin wadanda suka yarda da abin da ake yi da wadanda ke neman canji.”