✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dalilin da Birtaniya ta tsare Peter Obi

Ana zargin Obi da aikata wasu manyan laifuka.

An tsare dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar LP, Peter Obi a birnin Landan na kasar Birtaniya, lokacin da ya je yin bikin Easter kan zargin yin sojan gona.

A wata sanarwa da shugaban watsa labarai na yakin zaben Obi da Datti Mista Diran Onifade, ya fitar a ranar Laraba, ya ce jami’an shige da fice na Landan ne suka tsare Obi.

A cewarsa, Peter Obi ya isa filin jirgin sama na Heathrow da ke Landan daga Najeriya a ranar Juma’a 7 ga Afrilu, 2023, amma sai jami’an tsaro suka kama shi.

“An yi masa tambayoyi na tsawon lokaci kuma abin mamaki ne a ce an kama mutumin da ya yi rayuwa sama da shekara 10 a kasar.

“Babban laifinsa shi ne yin sojan gona wajen aikata manyan laifuka da aka alakanta su da sunansa,” in ji Onifade.

Onifade ya kara da cewa, Obi na fuskantar kalubale iri-iri, tun daga ranar 25 ga watan Fabrairun 2023 da aka gudanar da zaben shugaban kasa, inda ya zo na uku daga cikin ’yan takara 18.

Sai dai ya ce Obi na fuskantar matsin lamba tun da ya nuna cewar INEC ta tafka kurakurai a zaben da .

“Tunda aka ce ya garzaya kotu idan bai aminta da sakamakon zaben da aka yake fuskantar matsala.

“Ita kanta Gwamnatin Tarayya da ta nemi ya je kotu har tura ministan yada labarai Lai Mohammed zuwa kasar Amurka don shafa masa kashin kaji ka zargin cin amanar kasa.

“Haka ma layin wayar Obi ta samu matsala, wanda da ita aka yi amfani wajen lakaba masa laifi.

“Kamar dai ba su samu abin da suke so na tozarta shi ba ne, shi ya sa aka fara yi masa makarkashiya.”

Don haka ya ce Obi a shirye yake ya fuskanci duk kalubalen da Ubangiji ya rubuta masa.