✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dalilin da ban sake aure ba bayan shekara 12 da rasuwar Maryam —IBB

A’a, sam ban sake aure ba kuwa, da na yi ai da kowa ya sani.

Tsohon Shugaban Najeriya na mulkin soja, Ibrahim Badamasi Banbangida (IBB), ya bayyana dalilinsa na zama ba tare da sake yin wani auren ba tun bayan rasuwar matarsa, Hajiya Maryam Babangida.

A wata hira ta musamman da ya yi da gidan talibijin na Trust TV, IBB wanda a yanzu ya kai shekaru 80 a doron kasa, ya yi karin haske kan abubuwa da dama ciki har da wanda yake son ganin ya gaji kujerar Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a zaben 2023.

Ana iya tuna cewa, Hajiya Maryam Babangida ta riga mu gidan gaskiya a ranar 27 ta watan Disambar 2009, a lokacin tana da shekaru 60 cif a duniya.

Maryam wadda ita ce Uwargidan Shugaban Kasa a tsakanin shekarar 1985 zuwa 1993, ta rasu ne a Cibiyar Lafiya ta Johnsson da ke Jami’ar California a Jihar Los Angeles ta Kasar Amurka.

Rasuwar Maryam na zuwa ne bayan ta sha fama da cutar daji ta mahaifa.

Tun bayan rasuwarta yanzu shekara 12 ke nan, da dama daga cikin yan Najeriya sun yi tsammanin IBB zai sake auren wata matar da za ta taya shi zaman duniya amma har yanzu shiru a ke ji tamkar shuka da ci shurwa.

A wasu lokutan an yi ta yada jita-jitar cewa IBB zai sake aure, amma hakan bai tabbata ba kasancewar jita-jita ba ta kasancewa gaskiya.

Sai dai a yayin da wakilanmu suka tuntube shi game da batun yadda ya shafe shekaru ba tare da sake wani auren ba, IBB ya bayyana cewa, “A’a, sam ban sake aure ba kuwa, da na yi ai da kowa ya sani.

“Amma kuma har yanzu manema labarai ba su daina neman jin wannan labari ba, don har yanzu ana tuntuba ta a kansa.

“Saboda haka kowa ya sani cewa wannan ra’ayi ne na kashin kai na, na yanke shawarar hakan saboda na tabbatar da martabar mata ta, wanda dalilinsa nake zaune a matsayin wanda ba shi da aure, amma dai ba za a kira ni da tuzuru ba.”

A bayan nan ne tsohon shugaban kasar ya bayyana goyon bayansa ga Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo, ya tsaya takarar zaben shugaban kasa a 2023.

Babangida ya bayyana Osinbajo a matsayin mutumin kirki, kuma daya daga cikin ire-iren mutanen da Najeriya take bukata su mulke ta.

Ya jadadda goyon bayansa ga Osinbajo da cewa yadda Najeriya take shan fama, mutane na gari ne wadanda suka fahimci bambamcin da ke tsakanin al’ummar kasar kadai ne za su iya tafiyar da ita zuwa tudun mun tsira.

Ana iya kallon cikakkiyar tattaunawar da aka yi da IBB a shirin tuna baya da Trust TV za ta gabatar da misalin karfe 7.00 na yammacin ranar Lahadi.