✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dalilan da rikice-rikicen Kudancin Kaduna suka ki ci suka ki cinyewa

Kashe-kashen na ci gaba da gudana ne duk da kokarin da masu ruwa da tsaki suke yi.

A makon jiya fiye da mutum 40 ne suka rasa rayukansu a Kudancin Kaduna, ta hanyar sara da adduna ko harbi da bindiga ciki har da mata da kananan yara.

Kashe-kashen sun fi kamari ne a kananan hukumomin Kaura da Kauru da Zangon Kataf, sai ’yan kadan a kan iyakar Karamar Hukumar Jama’a da Kaura.

Baya ga rayukan da aka rasa an kuma yi asarar dukiyoyi na miliyoyin Naira da suka hada da gidaje da kayayyakin abinci da na kasuwanci da dabbobi masu yawa, tare da jefa daruruwan mata da magidanta da kananan yara zuwa gudun hijira a sansanin gudun hijira ko garuruwan dangi da ’yan uwa, inda sansanin gudun hijira na Zonkwa ke dauke da mutum 970 a lokacin hada wannan rahoto.

Kashe-kashen na ci gaba da gudana ne duk da kokarin da gwamnati da jami’an tsaro da kungiyoyi masu zaman kansu suke yi na shirya sulhu a tsakanin mazauna yankin musamman manoma da makiyaya da shugabannin al’umma da na addini da wakilan kungiyoyi daban-daban ta yadda za a shawo kan matsalolin tsaro da samun dawwamamen zaman lafiya a yankin.

A irin wadannan tarurrukan da aka soma tun shekarar 2017 an sha sanya hannu a takardun yarjejeniya a tsakanin manoma da makiyaya kan wasu kudirori da kowane bangare ya amince da su, amma hakan bai hana komawa gidan jiya ba, tare da zargin juna kan karya yarjejeniyar da suka rattaba wa hannu.

Abubuwan da aka fi maimaitawa a duk yarjejeniyoyin da ake kattabawa da har yau an kasa shawo kansu sun hada da bata gonakin manoma da makiyaya ke yi da toshe labin shanu da manoma ke yi, da kiwon da kananan yara da makiyaya ke yi da daukar doka a hannu da makiyaya ke zargin manoma na yi idan dabbobi sun shiga gonakinsu da kuma tare hanya ana kashe matafiyan da ba su san hawa ba, ba su san sauka ba, idan wata hatsaniya ta taso sai uwa uba hareharen daukar fansa da kowane bangare ke zargin juna da yi.

Har ila yau, takaddama kan batun mallakan filaye da gonaki a tsakanin Hausawan Zango da Katafawa da batun baki da ’yan kasa suna taimakawa wajen sabunta rikice-rikicen yankin.

Hukumar Zaman lafiya ta Jihar Kaduna (Kaduna Peace Commission) da Gamayyar Kwamitin Samar da Zaman Lafiya a Kudancin Kaduna (Southern Kaduna Joint Peace Committee); da Rabaran Yakubu Pam ya kafa kuma ta kunshi Hausawa da Fulani da sauran kabilun yankin da Kwamitin Hada-ka don Samar da Tsaro da Zaman Lafiya a Masarautar Atyap (Atyap Chiefdom Peace and Security Partnership Committee), wanda Sarkin Atyap Dominic Gambo Yahaya ya kafa da ke kunshe da Hausawa da Fulani da Katafawa da wasu kungiyoyi masu zaman kansu, sun sha shirya tarurruka a wurare daban-daban don samun zaman lafiya.

Harin da ya mayar da hannun agogo baya

Hari mafi girma da ake ganin ya sake farfado da hare-haren kwanakin nan, shi ne wanda aka kai yankin Kurmin Masara da ke Karamar Hukumar Zangon Kataf a ranar Lahadi 30 ga Janairun bana, inda aka kashe mutum 11 tare da kona gidaje 30 kamar yadda aka ruwaito a kafafen yada labarai.

Sai dai kafin wannan harin, a ranar 22 ga Janairun an samu rahoton kisan wani Bafulatani makiyayi a Gundumar Zaman Dabo wanda makasan suka gutsire kansa suka tafi da shi da kuma wanda aka sake kashewa kwana biyu bayan nan a Kasuwar Bakin Kogi da ke Karamar Hukumar Kauru da ke makwabtaka da Karamar Hukumar Zangon Kataf, wanda a wani hari da ake ganin na daukar fansa ne aka wayi-gari da kai mummunan harin a Kurmin Masara da za a dade ba a manta da shi ba.

Da yake amsa tambayar wakilinmu, Shugaban Kungiyar Ci-gaban Al’ummar Katafawa (ACDA) na Kasa, Mista Samuel Achi, ya ce ko da mene ne dalilan da ke sabbaba kashe-kashen nan ya kamata a tsaya haka nan domin abin ya yi yawa.

“Dole Fulani da Katafawa su dakatar da kashe-kashen nan haka.

“An zubar da jini mai yawa to, me kuma ake bukata? Mu sani ko mun ki, ko mun so dole muna bukatar juna, don haka lokaci ya wuce da za mu tsaya muna ta kashe kanmu da sunan mallakar filayen kakanni,” inji shi Shugaban ya bayyana rubibi da rigegeniyar mallakar kasa ne ke haddasa rigimar Hausawa da Katafawa, inda kowane bangare ke ikirarin gadonsa ne na iyaye da kakanni, yayin da su kuma Fulani makiyaya ke kukan rashin isasshen wurin kiwo.

A karshe ya yi kira ga gwamnati ta rika daukar matakin ba sani ba sabo, tare da zama ’yar ba-ruwanmu maimakon kallon da yawancin Katafawa ke mata na zuba ido ana kashe su ba tare da ta taba hukunta kowa a kai ba, sannan ya yi roko ga bangarorin da ba sa ga-maciji da juna su dakatar da daukar fansa haka nan.

Kakakin Kungiyar Fulani Makiyaya ta Miyetti Allah ta Kasa Reshen Jihar Kaduna, Ibrahim Bayero, ya ce abin da ya jawo sababbin hare-haren Kudancin Kaduna musamman na Masarautar Atyap da ke Karamar Hukumar Zangon Kataf shi ne harin 24 ga Janairun da ya gabata, inda wadansu matasa dauke da makamai suka ratso takanas daga Kurmin Masara a Zangon Kataf suka zo har kauyen Kizaga da ke makwabtaka da su a Karamar Hukumar Kauru, suka far wa wadansu Fulani makiyaya suka kashe su tare da fille kan daya daga cikinsu.

“Daga nan maharan suka ci gaba da bin gidajen makiyayan da ba su ji ba, ba su gani ba, inda suka kone gidaje biyu ciki har da yaro dan shekara daya mai suna Bilal Bukar da ya kone kurmus.

“Sannan sun sake kashe wani makiyayi dan shekara 19 a Ungwan Gankon da ke Gundumar Gora a Karamar Hukumar Zango Kataf ranar Asabar 29 ga Janairun bana yana cikin kiwo,” inji shi.

Ya ce, koka kan yadda aka kashe wani Bafulatani mai suna Aminu da ya saro ganyen bishiyar mangwaro don bai wa shanunsa a tsakanin kauyukan Zunuruk da Tsonje a tsakanin kananan hukumomin Kaura da Jama’a, “Hakan ya janyo bacewar shanu 25 bayan kashe 16,” inji shi.