✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Da sunan wace jam’iyya Yakubu Dogara ke zama a Majalisa?

Wata shida bayan sauya shekarsa, har yanzu ba a sanar a hukumance ba.

Tun bayan sauya shekar tsohon Shugaban Majalisar Wakilai, Yakubu Dogara, ake ta ja-in-ja tsakanin jam’iyyar PDP da ya baro da kuma APC mai mulkin da ya koma cikinta.

Yayin da ake ce-ce-ku-ce kan dalilin ficewarsa daga PDP zuwa APC, akwai kuma rashin tabbas kan jam’iyyar da yake a halin yanzu.

Shugaban Kwamitin Rikon Jam’iyyar APC na Kasa kuma Gwamnan Jihar Yobe mai ci, Mai Mala Buni ne ya sanar da sauya shekar Dogara bayan Bunin ya raka Dogara zuwa wata ganawa da Shugaba Buhari.

Har yanzu kuma ba a sanar da sauya shekar tasa ba kamar yadda aka sanar da sauya shekar sauran ’yan Majalisar da suka koma jam’iyyar APC daga APGA da wasu jam’iyyu a baya-bayan nan.

Ana gab da babban zaben 2019 ne Dogara, mai wakiltar Mazabar Dass/Bogoro/Tafawa Balewa ta Jihar Bauchi ya fice daga APC zuwa tsohuwar jam’iyyarsa PDP.

Dogara wanda ya tsaya kai da fata wajen kayar da APC a zaben 2019 ya bar ta ne saboda sabaninsa da Gwamnan Jihar Bauchi na lokacin, Mohammed Abdulllahi Abubakar.

Rikicin siyasar da ke tsakaninsu ce ta ba Sanata Bala Mohammed na jam’iyyar PDP damar cin zabe da kafa gwamnati a Jihar.

Baya cin zaben Bala Mohammed ne kuma tsohon Shugaban Majalisar Wakilan ya raba gari da shi har ta kai ya sake ficewa daga PDP.

Babu sunan Dogara a APC

A karar Dogara da wasu mutum hudu da PDP ta shigar na kalubalantar sauya shekar Dogara, APC ta shaida wa Babbar Kotun Tarayya cewa sunan Dogara ba ya cikin rajistar ’ya’yanta.

A jawabinsa, Shugaban Sashen Shari’a na APC, Dare Oketade, ya shaida wa kotun cewa ba shi da masaniyar dawowar Dogara cikinta kuma sunansa bai shiga cikin rajistarta ba.

Sauran mutanen da PDP ke kara a shari’ar mai lamba, FHC/ABJ/CS/1060/2020 ta hannun lauyanta, Jibrin S. Jibrin, su ne Shugaban Majalisar Wakilai, Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya (AFG), Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) da kuma APC.

Ya sauka daga kujerar da PDP ta ci zabe

PDP da Shugabanta PDP na Jihar Bauchi, Hamza Koshe Akuyam sun shaida wa Kotun cewa a karkashin inuwar jam’iyyar Dogara ya sake cin zaben komawa kujerarsa.

A cewarsu, tunda ya sauya sheka kamar yadda ya sanar da shugabanta a mazabarsa ta Bogor ‘C’ ta Jihar Bauchi a ranar 24 ga Yuli, 2020, ya makata ya sauka da kujerar da ya ci zabe a karkashin inuwar jam’iyyar.

Sun bayyana wa kotun cewa bisa tanade-tanaden Sashe na 68(1)(g) na Kundin Tsarin Mulkin Kasa, Dogara bai cancanci ci gaba da shiga harkokin Majalisar Wakilai a karkashin inuwa PDP da ya bari ba.

Shugaban jam’iyyar a Jihar, ya kara da cewa babu wani rikici ko rabuwar kai a reshen da zai iya zama hujjar Dogara na sauya sheka.

“Dogara ya rasa kujerarsa matsayinsa na Dan Majalisar Wakilai kuma bai cancanci halartar zama da sauran harkokin Majalisar Tarayya ba,  ko karbar karbar albashi ko alawus a matsayin dan Majalisar Tarayya,” inji takardar karar da suka shigar.

Ya ce a don haka, “Doka ta wajabta” wa Shugaban Majalisar Wakilai ya ayyana cewa an samu gibi a kujerar da Dogara ke kai sannan INEC ta gudanar da zaben cike gurbi.

Majalisa ta yi gum

Majalisar Wakilai dai ta ki cewa uffan kan sauya shekar tasa, har yanzu ba a sanar da sauya shekar tasa ba kuma hakan da Shugaban Majalisar, Femi Gbajabiamila ya yi ya saba al’adar Majalisar.

Bisa al’ada, mai jagorantar zaman Majalisa (Shugabanta ko Mataimakinsa) kan sanar da sauya shekar ’yan Majalisar a zauren Majalisar.

Amma an shafe watanni ba tare da an sanar da sauya shekar Dogara ba, ko karanta wasikarsa game da hakan.

Shi ma kuma ya yi gum a kan batun kuma ba a fiye jin duriyarsa sosai ba a Majalisar tun bayan saukarsa daga shugabancinta.

Ya kai APC ga nasara a zaben Bauchi

A baya-bayan nan, ya jagoranci yakin neman zaben da ya kai APC ga nasara a zaben cike gurbin Mazabar Dass ta Majalisar Dokokin Jihar Bauchi.

An yi zaben ne wata biyu da suka gabata domin cike gurbin marigayi Honorabul Mante Baraza wanda ’yan fashi masau garkuwa da mutane suka kashe shi a gidansa.

A baya-bayan nan kuma bangaren mata na APC a Jihar Bauchi ta jinjina masa tare da tabbatar da kasancewarsa a jam’iyyar.

Ina katin shaidarsa?

Wani jami’in APC a Bogoro, ya shaida wa wakilinmu ta waya cewa ba shi da tabbaci ko an ba wa Dogara katin shaidar zama dan jam’iyyar a mazabarsa.

Sai dai wani jami’in jam’iyyar a matakin jihar kuma ya shaida wa wakilin namu cewa Dogara dan jam’iyyar ce.

Ya kuma yi watsi da ji-ta-ji-tar rashin dawowarsa APC inda ya ce tuni tsohon Shugaban Majalisar Wakilan ya fice daga PDP.

Yanzu dai babu tabbas game da matsayin Dogara a tsakanin jam’iyyun biyu, wadanda kowacce daga cikinsu ya ci zabe a karkashin inuwarta.

Kawo yanzu dai bayani a hukumance, ko daga manyan jam’iyyun ko hukuncin da kotu ta zartar kan karar da PDP ta shigar a kansa ne zai yi alkalanci game da batun sauya shekar tasa.