✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Da sanin Ganduje Tinubu ya gana da Kwankwaso —Kofa

Kofa ya ce Ganduje da kansa ya shaida masa cewar yana da masaniyar ganawar Tinubu da Kwankwaso.

Zababben dan majalisar wakilai, Abdulmumin Jibrin Kofa, ya ce Gwamna Abdullahi Ganduje yana da masaniya game da ganawar da shugaban kasa mai jiran gado Bola Tinubu ya yi da Sanata Rabiu Kwankwaso a kasar Faransa.

Aminiya ta ruwaito yadda Tinubu da Kwankwaso suka yi ganawar sama da sa’o’i hudu a ranar Litinin.

A wani sautin waya da aka nada, an ji Ganduje yana bayyana rashin jin dadinsa kan ganawar Tinubu da Kwankwaso, inda ya ce ya yi hakan ne a kashin kansa.

An jiyo shi yana cewa ya kamata Tinubu ya tuntube shi ko kuma ya gayyace shi taron da ya yi da Kwankwaso.

Sai dai a zantawarsa da Aminiya, Kofa, wanda ya halarci ganawar da shugabannin biyu suka yi a Faransa, ya ce Ganduje ya tabbatar masa da cewa Tinubu ya tuntube shi kafin a yi taron.

“Na yi matukar kaduwa da na saurari sautin, amma ina ganin abu mafi muhimmanci shi ne ina son tabbatar muku cewa an tuntubi Gwamna Ganduje.

“Kuma shi da kansa ya tabbatar min cewa zababben shugaban kasar ya gayyace shi, ya kuma shaida masa cewa yana shirin ganawa da Kwankwaso, ya tambayi Ganduje ko ba ya son ya gana da Kwankwaso.

“Don haka babban rashin adalci ne ga shugaban kasa mai jiran gado, Gwamna Ganduje ya yi masa mummunan zato a gaban jama’a, alhali ya san cewa shugaban ya tuntube shi kafin wannan taron domin ya tabbatar min da hakan da kansa.

“Bai yi wa shugaban kasa mai jiran gado adalci ba, kuma ban yi imani cewa shugaban kasa zai yi watsi da duk wanda ya goyi bayansa ba… amma muhimmin abin shi ne hadin kan kasa da cigaban kasa.”