✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Crystal Palace ta nada Patrick Vieira a matsayin Manaja

Tsohon Kyaftin din na kungiyar Arsenal ya maye gurbin Roy Hodgson.

Crystal Palace ta nada Patrick Viera a matsayin sabon manajanta kan yarjejeniyar shekara a cewar wata sanarwa da kungiyar ta Firimiyar Ingila ta fitar ranar Lahadi.

Tsohon Kyaftin din na kungiyar Arsenal ya maye gurbin Roy Hodgson wanda ya ajiye aikinsa bayan shafe shekaru hudu yana jan ragamar horas da ’yan wasa.

Viera ya rattaba hannu kan kwangilar da za ta kai shi har zuwa karshen kakar wasanni ta shekarar 2024, inda zuwansa kungiyar ya zamo karo na uku a matsayin babban manaja.

A baya bayan nan ya jagoranci kungiyar Nice da ke buga gasar Ligue a Kasar Faransa, inda a watan Dasumbar bara ta raba gari da shi saboda rashin tabuka abin kirki.

A tsakanin shekaru biyu da rabi da ya shafe tare da ita, Viera ya jagoranci kungiyar ta kammala gasar Ligue a mataki na bakwai da kuma na biyar.

A lokacin da yake murza leda, Viera wanda ya shafe tsawon shekara 9 a Arsenal, na daya daga cikin ’yan wasan da suka yi shura a karkashin jagorancin Arsene Wenger.

Ya lashe Firimiyar Ingila uku, ciki har da kakar da Arsenal tashafe ba tare da an doke ta ba a gasar.