✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

COVID-19: Gwamnatin Filato na takaicin masu watsi da kariya

Gwamnatin jihar ta ce tilas ne jama’a su koma amfani da takunkumi.

Gwamnatin Jihar Filato ta koka kan yadda mutane a jihar ke yin watsi da matakan kariyar cutar coronavirus.

Kwamishinan Yada Labaran Jihar, Dan Manjag, ya bayyana hakan, inda ya ce mutane da dama ba sa amfani da takunkumi.

Kwamishinan ya ce dole ne gwamantin jihar ta wajabta wa mutanen jihar bin dokokin kariya da aka tanadar.

A taron masu ruwa da tsaki na jihar da ya gudana a ranar Laraba, gwamnatin jihar ta amince da rage cunkoson mutane a da kaso 50 cikin 100.

Sannan ta dakatar da dukkanin shagulgula a yayin bikin Kirsimeti, ta kuma wajabta sanya takunkumi da kuma kaurace wa taron mutane.

Gwamantin jihar ta kuma ba wa masu ruwa da tsakin umarnin wayar da kawunam al’umma tun daga tushe, don dakile bazuwar cutar a karo na biyu.