✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

COVID-19 :Gwamnan Legas ya ba da damar cin kasuwa a kullum

Gwamnan Jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu ya ba da izinin bude daukacin kasuwanin jihar ta yadda za su rika ci a kowace rana maimakon a baya…

Gwamnan Jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu ya ba da izinin bude daukacin kasuwanin jihar ta yadda za su rika ci a kowace rana maimakon a baya da aka takaita ranakun bude su sakamakon annobar COVID-19.

Sanarwar da Kwamishinan Kananan Hukumomi da Al’amuran Jama’a, Wale Ahmed, ya fitar a ranar Talata 27 ga watan Oktoba, ta ce yanzu daukacin kasuwannin kayan abinci da ma wadanda ba na kayan abinci ba za su iya ci a kullum sabanin yadda a baya aka takaita bude su zuwa kwanaki uku a mako.

A baya dai an kayyade ranakun bude kasuwanin a fadin jihar Legas ne domin kare yaduwar annobar COVID-19, amma wannan sanarwar ta kawo karshen tsarin takaita ranakun cin kasuwa a Jihar Legas.

A watan Fabrairun 2020 ne aka fara samun bullar cutar COVID-19 a Najeriya bayan wani dan kasar Italiya ya shigo kasar ta filin jirgi na Murtala Mohammed da ke Legas.

Daga baya yaduwar cutar a kasar kamar yadda aka yi ta samu a sauran kasashen duniya ta tilasta hukumomi sanya dokar takaita zirga-zirga da taruwar jama’a a kasuwanni, makarantu, wuraren ibada da sauran wuraren taruwar jama’a.

Jihar Legas ta zama cibiyar cutar a Najeriya wajen yaduwar cutar da yawan wadanda suka mutu, kafin daga bisani lamarin ya fara lafawa.

Yanzu jihar da sauran jihohin Najeriya sun sassauta dokokin kariyar cutar.