✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Coronavirus ta kashe mutum 39 a China

Shi ne adadi mafi yawa da aka samu tun tsaurara dokar kulle makonni hudu da suka gabata.

Akalla mutum 39 ne suka riga mu gidan gaskiya sakamakon annobar Coronavirus a birnin Shanghai na China mai hada-hada a ranar Asabar.

BBC ya ruwaito cewa wannan shi ne adadi mafi yawa da aka samu tun tsaurara dokar kulle makonni hudu da suka gabata.

A ranar Litinin da ta gabata aka ba da rahoton mutum na farko da ya mutu tun sake dawowar annobar, da kuma samun dubbai da suka kamu a rana guda.

Birnin Shanghai mai al’umma miliyan 25 yanzu haka na fama da barkewar wannan annoba mafi girma a China kawo yanzu.

Ana ci gaba da daukar matakai masu tsauri, da kwashe mutane daga gidajensu domin yi feshi.

Sannan a Beijing, jami’ai na gargadi kan barazanar da cutar da ke yaduwa cikin gaggawa ke haifarwa.