✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Coronavirus: An samu sabbin kamuwa 48

An samu karin wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar coronavirus mutum 49 a Najeriya. Ashirin da uku daga cikinsu a jihar Legas suke, 12…

An samu karin wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar coronavirus mutum 49 a Najeriya.

Ashirin da uku daga cikinsu a jihar Legas suke, 12 a Yankin Babban Birnin Tarayya, 10 a Kano, biyu a Ogun, daya a Oyo.

Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa ta Najeriya (NCDC) ce ta bayyana hakan a wani sako da ta wallafa a shafinta na Twitter.

“Zuwa karfe 10.40 na daren 18 ga watan Afrilu akwai mutum 541 wadanda aka tabbatar sun kamu da COVID-19 a Najeriya”, inji hukumar.

Ta kuma ce a cikin wannan adadi an sallami mutum 166 wadanda suka warke, yayinda mutum 19 suka riga mu gidan gaskiya.