✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Cire Tallafin Mai: An rage ranakun zuwa aiki zuwa kwana 3 a Kwara

Gwamnatin ta yanke hukuncin ne don rage wa ma'aikatan jihar radadi.

Gwamnatin Jihar Kwara ta rage kwanakin zuwa aikin ma’aikatanta a matsayin matakin wucin-gadi na  rage musu radadin cire tallafin man fetur da Gwamnatin Tarayya ta yi.

Shugabar ma’aikatan jihar, Misis Susan Modupe Oluwole, ta sanar cewar Gwamna Abdulrahman Abdulrazaq ya bayar da umarnin rage kwanakin zuwa aiki zuwa kwana uku a mako ga kowane ma’aikaci.

Sanarwar da babban sakataren yada labarai, Murtala Atoyebi ya fitar, ta umarci dukkan shugabannin ma’aikatu da hukumomin gwamnatin jihar da su gaggauta tsara yadda tsarin zai yi aiki.

Sai dai shugabar ma’aikatan ta gargadi ma’aikatan da kada su yi wasa da damar sannan ta  jaddada cewa za a kara sanya ido kan vadda suke gudanar da ayyukansu domin tabbatar da bin doka da oda.

Tun bayan da Shugaba Tinubu ya sanar da cire tallafin man fetur a jawabinsa na karbar mulki aka fara samun dogayen layuka a gidajen mai, da kuma tashin gwauron zabon farashin man.

Hakan dai ya jefa mutane cikin tsaka mai wuya musamman a fannin sufuri.