✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

CIKIN HOTUNA: Irin barnar da fashewar ammonium ta yi a Lebanon

Sama da mutum 100 ne suka mutu yayin da dubbai suka jikkata a Beirut babban birnin Lebonon, bayan wata mummunar fashewa. A wani rahoto da…

Sama da mutum 100 ne suka mutu yayin da dubbai suka jikkata a Beirut babban birnin Lebonon, bayan wata mummunar fashewa.

A wani rahoto da BBC ta wallafa na cewa, Shugaban kasar Michel Aoun ya ce ton fiye da 2,750 na sinadirin Ammonium nitrate da aka ajiye a wata ma’adana na shekaru shida ne ya janwo wannan barna.

Masu aikin ceto na kokarin gano wadanda suka makale a wurin da abin ya faru.
Sojoji sun hako wani mutum da ya makale a karkashin gini. Hoto: AFP.
Jirgin sojin Lebanon na shawagin duba irin barnar da ta faru. Hoto: Reuters.
Wani mutum yana duba barnar da lamarin ya yi a wani gida a Beirut. Hoto: Reuters.
Gabar teku a a Beirut inda aka samu fashewar sunadarin na Ammonium nitrate.
Wasu jiragen ruwa ke ci da wuta a gefan teku da ke Beirut
Wani bangare na Beirut inda fashewar ammonium nitrate ta shafa. Hoto: AFP
Yadda lamarin na ranar Talata ya yi barna a assa na birnin Beirut. Hoto: AFP.
Yadda wasu gine-gine suka rushe bayan fashewar sunadarin a Beirut. Hoto: AFP.