✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Chloroquine na sha yayin jinyar coronavirus –Gwamnan Bauchi

Gwamnan jihar Bauchi Sanata Bala Abdulkadir Mohammed ya ce lokacin da ya kamu da cutar coronavirus ya sha kwayoyin maganin Chloroquine da Zithromax ne ya warke, saboda…

Gwamnan jihar Bauchi Sanata Bala Abdulkadir Mohammed ya ce lokacin da ya kamu da cutar coronavirus ya sha kwayoyin maganin Chloroquine da Zithromax ne ya warke, saboda haka ya yi umurni a rika jinyar masu cutar da wadannan magunguna.

Gwamna Bala Mohammed ya ba da wannan umarni ne lokacin da yake amsa tambayoyin manema labarai a Bauchi bayan da ya ba yi karin haske game da halin da ake ciki a yaki da cutar a jihar.

Ya ce shi ne zai “dauki alhakin duk abin da ya faru sakamakon amfani da kwayoyin kuma a gaskiya kwararrun likitocinmu na yin amfani da wadannan kwayoyin magunguna don jinyar  masu cutar duk da cewa wadansu likitoci ba su amince a yi amfani da su ba”.

Ya  kara da cewa tun da shi ne gwamnan jihar Bauchi ba ya so wani ya mutu, don haka hakkinsa ne ya dauki matakin da ya tabbatar zai kare rayuka da dukiyoyin jama’a.

Gwamnan ya ce ya umarci jami’an kula da lafiya su yi amfdani da irin magungunan da suka ba shi da kuma wanda suke bai wa wadanda aka yi jinyarsu suka warke a jihar domin yi wa mutane jinya.

Jikin bakar fata

“Maimakon a ce yana da illa a ki sha a mutu gara a sha a warke don mu bakaken fata jikinmu na daukar kwayar maganin, kuma a nan kasar da ma mun saba muna shan kwayar Chloroquine ba ta cutar da jikinmu, kuma dukkan wadanda suka warke daga cutar a nan Bauchi maganin suka sha kuma ba wanda ya rasa ransa ko da mutum guda.

“Kuma a yau dukkan masu dauke da cutar su 23 ba wanda ya nuna ko da alamun jikkata”, inji gwamnan.

Kalaman gwamnan tamkar kara azama ne wa muhawarar da ake yi a duniya a kan ingancin Chloroquine.

Ko da shugaban Amurka Donald Trump ma a kwanakin baya ya ce kwayar maganin na kawar da cutar, an soki kalamanshi da cewa maganin bai bi dukkan matakan kula da magunguna da ake bukata ba kafin a ce shi ne zai warkar da cutar; mai yiwuwa yana da wata illa da ba a sani ba.

Maganin annobar

Gwamna Bala Mohammed ya kuma bayyana cewa rufe jihar kirif ba shi ne maganin matsalar ba illa iyaka mataki ne dake wahalar da jama’a.

“Ko da jihohin da suka rufe kirif din ma cikin wahala suke haka ma alummarsu, amma idan mutanenmu suka ki ba da tazarar da ta kamata wato social distance muka ga abin zai munana za mu rufe jihar kirif”, inji shi.

Ya kuma ce, “kwararrun likitocinmu da kuma masu wayar da kan al’umma dukansu suna iyakacin kokarinsu wajen gano wadanda ake zaton suna dauke da cutar kuma suna tantance mutanen da suka yi mu’amala da masu cutar; ina gani yin haka da daukar matakan kariya daga kamuwa da cutar su ne hanyoyin da za a bi don samun sauki”.

Cibiyoyin gwaji

Gwamnan ya ce tare da taimakon Hukumar Raya Yankin Arewa Maso Gabas zai kafa cibiyoyin daukar samfurin wadanda ake zato suna dauke da cutar domin samun saukin tantace su kuma za a kafa cibiyoyin guda biyu ne a Bauchi da Azare.

“Idan an kafa wadannan cibiyoyi a jihar Bauchi ko wace rana za a iya tantance mutum 1,000.

“Za mu kafa wannan cibiya a Bauchi da Azare ne domin kafa ta Azare na da muhimmanci domin tana kan iyaka da jihohin Kano da Borno da kuma Jigawa”, a cewarsa.

Gwamna Bala ya ce gwamnatinsa ta samar da dukkan abubuwan da ake bukata a wuraren da ake bukata.

“Mun samar da gadaje 100 a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa dake Bauchi, an kuma samar da gadaje 120 a Asibitin Bayara, an samar da gadaje 80 a Asibitin Gwamnatin Tarayya da ke Azare”, sannan ya ce kuma tare da hadin gwiwar bankin Zenith sun kara sanya gadaje 100 a Toro.

Gwamnan ya ce jihar Bauchi tana da fiye da abin da ake bukata na tantace mutane da dama da kuma yin jinyarsu in sun kamu da cutar.