✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

CBN ya umarci bankuna su ba da sabbin kudi ta kan kanta

CBN ya kayyadde ba wa kowane kwastoma Naira 20,000 na sabbin kudaden a kullum

Babban Bankin Najeriya (CBN) ya umarci bankuna su fara ba wa ’yan Najeriya sabbin takardun Naira da aka sauya wa fasali a saman kanta.

Umarnin na CBN ya kayyadde ba wa kowane kwastoma Naira 20,000 na sabbin kudaden a kullum, kamar yadda Darakan yada Labaran bankin, Osita Nwanisobi, ya sanar a safiyar Alhamis.

Hakan na zuwa ne bayan guna-gunin ’yan Najeriya kan karancin sabbin takardun kudaden a hannunsu, alhali sun riga sun kai akasarin tsoffin da ke hannunsu bankuna domin gudun cikar wa’adin tsoffin da CBN ya sanar a baya.

Batun karancin sabbin takardun kudaden dai ya kawo cikas ga harkokin kasuwanci, a yayin da ’yan Najeriya ke shafe awanni suna bin layi domin cira daga ATM, inda a karshe ma wasu ba sa samu.

Hakan ya ba da dama ga masu harkar POS, inda suke cin kasuwa, tare da kari a kan cajin da suke karba a kan masu neman sabbin kudaden a hannunsu.

Daga baya hatta tsoffin kudin rububin neman su ake yi, damar da masu hada-hadar kudi ke amfani da ita wajen tatsar al’umma.

CBN dai sun nuna damuwa game da ayyuka masu sayar da sabbin kudaden da kuma masu yin liki da kudi a wuraren bukukuwa.

Sun kuma jaddada cewa za su ci gaba da aiki da hadin gwiwar hukumomin FIRS, EFCC da NFIU domin maganin masu yin hakan.