✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Canji kudi: Manoma sun ki sayar wa ’yan kasuwa amfanin gona

Manoma na komawa gida da amfanin gona da suka kai kasuwa saboda rashin masu tsabar kudi

Manoma na kin sayar da amfanin gona ga ’yan kasuwar da ke son tura musu kudin kayansu da suka saya ta bankin, saboda karancin takardun kudi.

Aminiya ta gane wa idonta yadda manoma ke komawa gida da amfanin gona da suka je sayarwa a kasuwa saboda rashin masu tsabar kudi a babbar kasuwar hatsi da ke Saminaka a Jihar Kaduna.

Wani manomi, Abdullahi Nasiru, ya shaida wa Aminiya cewa ya kawo farin wake da masara kasuwar, amma babu mai saya saboda karancin takardun kudade.

Ya ce, “Akwai masaya da suke zuwa don su tura kudade ta asusun ajiyar banki, a amma mu ba za mu amince ba, domin idan aka tura mana ta banki, ba za mu sami takardun kudaden ba.

“Gaskiya yanzu muna cikin halin kunci, don idan aka ce kasa babu kudi ai dole a shiga halin kunci, domin komai zai tsaya kamar yadda ta kasance a yanzu; Muna shawartar gwamnati, don Allah su sakar mana kudin nan.”

’Yan kasuwa sun shiga saka-mai wuya

Bincikenmu ya gano baya ga manoman, ’yan kasuwa ma da suka je babbar kasuwar hatsin domin sayen amfanin gona sun shiga mawuyacin hali, saboda karancin sababbin takardun kudaden da aka canza.

Bashir Magaji mai sayen kayan amfanin gona ne da yazo wannan kasuwa daga Kano, ya shaida wa Aminiya cewa, “Gaskiya yau kasuwa babu dadi, domin duk wanda bai zo da kudi ba, sayen kayan amfanin gona zai yi masa wahala.”

Ya ce dalili shi ne masu sayen kaya, “ba su zo da kudi ba domin suma a can ba su da kudin, domin duk inda kaje ko wurin masu POS ne babu kudi.

“Gaskiya a yanayin yadda nake zuwa wannan kasuwa na sayi kaya a duk ranar kasuwar, zan iya cewa a yau ban sayi kaya ba.

“Duk ranar kasuwa nakan zo na sayi kaya buhu 30 zuwa buhu 50, amma yau buhu shida na saya.

“Gaskiya wannan hali ya sanya mutane cikin damuwa, mutum da kudinsa amma ya kasa amfanin da su,” in ji shi.

Ana cin kwakwa

Wani manomi, Abdullahi Nasiru, ya shaida wa Aminiya cewa ya kawo farin wake da masara kasuwar, amma babu mai saya saboda karancin takardun kudade.

Ya ce, “Akwai masaya da suke zuwa don su tura kudade ta asusun ajiyar banki, a amma mu ba za mu amince ba, domin idan aka tura mana ta banki, ba za mu sami takardun kudaden ba.

“Gaskiya yanzu muna cikin halin kunci, don idan aka ce kasa babu kudi ai dole a shiga halin kunci, domin komai zai tsaya kamar yadda ta kasance a yanzu; Muna shawartar gwamnati, don Allah su sakar mana kudin nan.”

Shi ma da yake zantawa da Aminiya, wani dillali a kasuwar, Malam Maiwada Dagi Saminaka, ya bayyana cewa ba su taba shiga irin wannan hali na tsaka mai wuya a kasuwar ba.

“Mutane kowa ya kawo kaya yana bukatar kudi, don biyan bukatarsa yana tsaye, amma ko kwabo ba mu samu ba.

“Na zo wannan kasuwa tun karfe 6 na safe, amma har yanzu ban sayar da komai ba. Kowa babu kudi a hanunsa.

“Wannan tsanani ya kai tsanani; Don haka muna fata Allah Ya kawo mana sauki.

“Manoma sun shiga cikin tashin hankali, sakamakon wannan al’amari. Kowa yana bukatar ya sayi wani abu. Akwai wanda bai taba zuwa banki ba, amma yanzu an ce sai ya je.

“Don haka ga kayan nan ba a sayar da komai ba.Wannan babbar matsala ce, a wurin talaka, sai dai muna rokon Allah, Ya kawo mana sauki,” in ji shi.