✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buratai ya ziyarci sojojin da suka ji rauni a yaki da Boko Haram

Ya kuma kaddamar da ayyuka a babban Asibitin Sojoji na 44

Shugaban Rundunar Sojin Kasa ta Najeriya Laftana-Janar Tukur Yusuf Buratai, ya ziyarci Asibitin Sojoji na  44 da ke Kaduna inda ya duba dakarun da suka ji rauni a yaki da Boko Haram da ’yan bindiga.

Buratai ya kuma duba wasu daga cikin ayyukan da ake aiwatarwa a asibitin tare da kaddamar da wadanda aka kammala a barikin sojin.

A ganawarwsa da manema labarai bayan ziyarar, Daraktan Hulda da Jama’a na Rundunar, Birgediya Sagir Musa, ya bayyana cewa sun zo dubiyar ne don ganin dakarun Operation Lafiya Dole da Operation Sahel Sanity da suka ji rauni a filin daga da ake jinyar su a asibitin.

“Har-ila-yau ziyara ce ta duba ayyukan da aka kammala na sabunta wasu kayayyakin aiki da ke da bukatar sabuntawa a Asibitin Sojoji na 44 da ke Kaduna,” inji Sagir.

Aminiya ta rawaito cewa a ranar Litinin Kwamitin Lamurran Sojin Kasa na Majalisar Dattawa ya kai makamnaciyar ziyarar a Asibitin Sojoji da ke Maiduguri inda Sanata Suleiman Abdulkadir ya yi kira da gwamnatocin jihohi da su samar wa sojojin ayyukan yi.

Akalla sojoji 416 da suka jikkata a wurin yuki da ’yan ta’addan Boko Haram a Jihar Borno ne ake jinyar su a.