✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Burin ’yan mata masu yi wa kasa hidima

Kamar kowa, ’yan matan masu yi wa kasa hidima na da buri. Ga biyar daga cikin manyan burace-buracensu

Babu tantama duk masu yi wa kasa hidima sun kammala wata babbar makarantar gaba da sakandare kuma suna da burace-burace da suke son cikawa bayan sun gama yi wa kasa hidimar.

Samun aiki ba shi ne kadai burinsu a rayuwa ba, musamman ’yan matan cikinsu.

Shin ko wadanne burace-burace ne ’yan mata masu yi wa kasa hidima ke da su?

Aminiya ta ji ta bakin wasu daga cikinsu, ga kuma biyar daga cikin burace-buracensu:

1- Aure:
Buri na farko da dukkan ’yan matan da muka zanta da su suka yi ittifaki a kai shi ne aure.

Musamman Zara Idris na da burin ganin kafin ta kammala yi wa kasa hidima ta yi aure.

Dalilinta na kulla wannan buri a zuciyarta shi ne ta raya Sunnah.

“Ina so na raya Sunnah, na bauta wa Allah, na kuma samu zuri’a ta-gari, wadda zan yi alfahari da ita Ranar Gobe”, inji ta.

2- Samun aiki:
Buri na biyu da ’yan matan suka yi ittifaki a kansa shi ne samun aiki kafin su kammala yi wa kasa hidima.

A cewar Aisha Ibrahim, misali, tana son ta yi aiki ne don ta taimaka wa al’ummar kasa baki daya.

“Ina so na yi aiki don na taimaka wa al’umma, musamman ’yan uwa da abokan arziki ta hanyar dauke musu wasu nauye-nauye”, inji ta.

3- Karo ilimi:
Masu iya magana kan ce “karamin sani kukumi”.

Mai yiwuwa wannan ne ya sa tun ma kafin su kammala karatunsu na gaba da sakandire, wasu daliban ke fatan zuwa su karo ilimi, musamman su yi digiri na biyu.

Wasu kuma ganin yadda aiki ke wahala, sukan gwammace su je su kara karatu, ko ba komai sun samu karin ilimi wanda ka iya ba su karin dama.

Zainab Mika’il na cikin masu irin wannan burin.

“So nake na koma makaranta saboda yanzu aiki na wahala. Don haka da na zauna jiran aiki gara kawai na koma na karo karatu”, inji ta.

4- Biyan bukata:
Babu shakka ko wanne dan-Adam yana fata wata bukatarsa a rayuwa ta biya.

Su ma ’yan mata masu yi wa kasa hidima suna da wasu abubuwa da suke bukata suke fata bukatar za ta biya.

Alal misali, Hamra Ibrahim ta dade tana sha’awar wake-wake, don haka ta wayi gari tana da bukatar ta zama mawakiya, in so samu ne ma kafin ta kammala hidimar kasa.

“Ina da burin zama mawakiya saboda duk lokacin da na ji waka sai na ji farin ciki; ko da ina cikin bacin rai ne waka tana nishadantar da ni, kuma tana debe min kewa ko damuwa, sannan tana sa ni dariya a ko da yaushe”, inji Hamra.

Wannan ne ya sa take so ta fara wakar da kanta.

5- Yin fice:
Wasu ’yan matan masu yi wa kasa hidima na da burin su shahara a cikin al’umma.

Hakan ne ma ya sa Hafsat Salisu ke fatan zama jarumar fina-finan Hausa, in da so samu ne, kafin ta kammala yin hidimar kasa.

“Ina matukar sha’awar wasan kwaikwayo. A duk lokacin da na kalli wasan kwaikwayo sai na ji dadi a raina, na ji ina ma ni ce na shahara haka”.

Hafsat ta kuma ce zama jarumar fina-finan Hausa zai sa ta zama abar alfahari ga mutane da dama.