✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buni ya yi ganawar sirri da kwamitin babban taron APC

Buni ya ce saura kiris su kammala shirin gudanar da babban taron APC yadda aka tsara

Gwamnan Jihar Yobe kuma Shugaban Kwamitin Riko da Tsare-Tsaren Babban Taron Jam’iyyar APC, Mai Mala Buni, ya yi ganawar sirri a cikin dare da mambobin kwamitin, jim kadan bayan dawowarsa Najeriya.

Buni ya bayyana cewa kwamitin na gab da kammala shirye-shiryen babban taron jam’iyyar da za a gudanar a ranar Asabar mai zuwa, 26 ga watan Maris.

Buni ya bayyana haka ne yayin wata tattaunawa da manema labarai a Abuja a daren ranar Alhamis, lokacin da Gwamna Abubakar Sani Bello na Jihar Neja da Gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello, da wasu ’yan jam’iyyar suka kai masa ziyarar goyon baya.

Gwamna Sani Bello ya zama mukaddashin shugaban APC bayan Buni ya yi tafiya zuwa kasar waje na tsawon kwanaki 17 don ganin likita.

Lamarin da ya haifar da sa-toka-sa-katsi game da matsayin Buni a jam’iyyar, wasu na cewa korar shi aka yi, wasu muka na cewa ya mika wa Gwamna Bello ragama ne a matsayin mukaddashi.

Saura kiris mu kammala shiri —Buni

Amma da yake jawabi, Buni ya bayyana cewa, “Tun da na yi tafiya jam’iyya ba ta tsaya ba, Mai Girma Gwamna ya yi kokari sosai wajen tafiyar da al’amuran jam’iyya.

“Mun zo nan ne don tattauna batutuwan da ke gabanmu, yanzu muna dab da kammala shirye-shiryen gudanar da babban taronmu na kasa a ranar 26 ga watan Maris.

“Mun hada kai domin cimma nasara wajen kammala wannan aiki, ina so in jaddada cewa za a gudanar da babban taronmu na kasa,” inji Buni.

Ina Sakataren Jam’iyya?

Dangane da rashin halartar taron da Sakataren Kwamitin Rikon APC, Sanata John James Akpanudoedehe, Buni ya bayyana cewa, “Kun san cewa wannan ba taron kwamiti ba ne.

“Wadannan mambobin Kwamitin Riko da Shirya Babban Taro da kuka gani sun zo ne domin kawo min ziyara tare da yi mi  fatan alheri bayan dawowa daga jinya da na yi a kasar waje, don haka ba taro ba ne da za a tambayi dalilin halartar sakatare, ko yau ya kawo min ziyara.”

Gabanin dawowar Buni, a ranar Alhamis aka fitar da wata takarda da Gwamna Bello da sauran mambobin kwamitin babban taron, in banda Buni, suka sanya hannu cewa sun dakatar da Sanata Akpanudeodehe, saboda rashin iya kamun ludayinsa.

A yake nasa jawabin a lokacin da suka ziyarci Buni, Gwamna Sani Bello, ya ce, tun “a makon da ya gabata mun sanar da cewa muna dab da gudanar da babban taron APC.”

Daga karshe mambobin kwamitin rikon sun yi wata ganawar sirri wanda ba su bar manema labarai sun shiga ko sanin abin da suka tattauna ba.