✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari zai kai ziyara Borno

Ziyara ta karshe da Buhari ya kai Jihar Borno an yi masa ihun ba ma yi.

A yau Alhamis Shugaban Kasa Muhammadu Buhari zai kai ziyara Jihar Borno da ke Arewa maso Gabashin Kasar.

Wannan na kunshe cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun Sakataren Yada Labarai na Fadar Gwamnatin Jihar, Isa Gusau ya fitar.

Sashen Hausa na BBC ya ruwaito Gwamna Babagana Zulum yana rokon yan jihar da su bayar da goyon baya da fatan alheri a yayin ziyarar.

Sanarwar ta ce daga cikin dalilan ziyarar Shugaba Borno akwai kaddamar da wasu ayyukan ci gaba da gwamnatin Jihar ta aiwatar.

Sannan shugaban zai duba yanayin tsaron da yankin Arewa maso Gabas yake ciki.

Haka kuma, shugaban zai kaddamar da rukunin farko na gidaje 10,000 wadanda ya amince a gida domin sake tsugunar da yan gudun hijira.

Borno ce jihar da ta zama hedikwatar kungiyar Boko Haram inda ake fama da hare-haren mayakan.

Ziyara ta karshe da Shugaba Buhari ya kai Jihar Borno ita ce ranar 12 ga watan Fabrairun 2020, inda aka samu wani dandazo na mutane da suka yi masa ihun “ba ma yi, ba ma yi.”