✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari ya yi ta’aziyyar tsohon shugaban kasar Zambiya

Shugaba Banda ya rasu yana da shekara 85 a duniya.

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, ya aike da sakon ta’aziyyarsa ga gwamnati da kuma daukacin al’ummar kasar Zambiya kan rasuwar tsohon shugaban kasar, Rupiah Bwezani Banda.

Banda ya rasu yana da shekara 85 a duniya.

Sakon na cikin wata sanarwa da hadiminsa kan kafafen watsa labarai, Garba Shehu ya fitar a ranar Talata, zuwa ga Shugaba Hakainde Hichilema na Zambiya.

Buhari ya bukaci shugabanni a Afirka su yi koyi da kyawawan halaye irin na marigayi shugaba Banda wajen martaba tsarin dimokuradiyya.

Shugaba Banda ya sauka daga mulki a 2011 sannan ya jagoranci mika mulki a kasar a 2021.

Buhari ya yi addu’ar samun ci gaba da waraka daga rashin shugaba Banda ga iyalansa.

An shirya bikin binne gawar Mista Banda a ranar 17 ga watan Maris, 2022.