✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari ya yi ganawar sirri da Shugaban Ghana

Shugaba Muhammadu Buhari ya yi ganawar sirri da takwaransa na Ghana, Nana Akufo-Addo ranar Alhamis a fadar Shugaban  Kasar da ke Abuja. Kamfanin Dillancin Labarai…

Shugaba Muhammadu Buhari ya yi ganawar sirri da takwaransa na Ghana, Nana Akufo-Addo ranar Alhamis a fadar Shugaban  Kasar da ke Abuja.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN), ya ce ya zuwa lokacin rubuta rahoton nan babu karin haske kan ajendar ganawar shugabannin biyu.

Koda yake NAN din ya ruwaito cewa Shugaba Addo wanda shi ne Shugaban Hukumar Shugabannin Kasashen yammacin Afirka (ECOWAS), ya kai ziyarar ce da zimmar tattaunawa kan batutuwan da suka jibanci yankin da Shugaba Buhari.

Bayanai sun ce Shugaban na Ghana ya yi amfani da damar wajen jajanta wa gwamnati da al’ummar Najeriya kan mutuwar Babban Hafsan Sojin Kasa, Laftanar-Janar Ibrahim Attahiru tare da wadansu jami’an sojin guda 10 a Jihar Kaduna cikin makon jiya.