✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Buhari ya taya Shugaban China Xi Jinping murnar lashe zabe

Buhari ya yi amanna cewa makomar kawancen Najeriya da China za ta ci gaba da bunkasa.

Shugaba Muhammadu Buhari ya taya Shugaban China, Xi Jinping murnar sake lashe zabe karo na uku.

A Juma’ar makon jiya ce Majalisar Dokokin China ta kada kuri’ar sake bai wa Shugaba Xi damar mulkar kasar na tsawon wa’adin shekaru biyar a matsayin Shugaban Kasa kuma jagoran Rundunar Sojan China (CMC).

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya NAN ya ruwaito cewa, sakon taya murnar na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa Femi Adesina ya fitar a ranar Lahadi.

Sanarwar ta ce a karkashin shugabancin Xi, dangantaka tsakanin China da Najeriya, wadda aka fara tun a shekarar 1971 a lokacin da kasashen biyu suka kulla huldar diflomasiyya a hukumance, ta bunkasa cikin sauri a harkokin kasuwanci da hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu.

Buhari ya yi amanna cewa makomar wannan kawancen da China za ta ci gaba da bunkasa cikin sauri a fannonin soja, siyasa, kasuwanci, hada-hadar kudi, huldar mai da iskar gas, da ma hadin gwiwa a fannin sadarwa, noma da ababen more rayuwa da kuma masana’antu.

Shugaba Buhari ya yi wa Gwamnatin China da jama’ar kasar fatan samun zaman lafiya, ci gaba da wadata a karkashin jagorancin Shugaba Xi.