✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari ya shiga ganawar sirri da Majalisar Tsaro ta Kasa

Shugaba Buhari a halin yanzu yana jagorantar zaman Majalisar Tsaro ta Kasa.

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya shiga bayan labule tare da Majalisar Tsaro ta Kasa a fadar Gwamnatinsa ta Villa da ke birnin Abuja.

Wadanda suka albarkaci taron sun hadar da Mataimakin Shugaban Kasa Farfesa Yemi Osinabajo; Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha; Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa, Farfesa Ibrahim Gambari da Ministan Shari’a kuma Lauyan Koli na kasa, Abubakar Malami.

Sauran Mahalarta taron sun hadar da Ministan Tsaro, Manjo Janar Bashir Salihi Magashi mai ritaya; Ministan Harkokin Cikin Gida, Rauf Aregbesola; Ministan Harkokin ’Yan Sanda, Muhammadu Dingyadi da Babban Mai Ba da Shawara kan Harkokin Tsaron Kasa, Manjo Janar Babagana Monguno mai ritaya.

Shugabannin Tsaro da suke halartar taron sun hada da Shugaban Ma’aikatan Dakarun Soji, Janar Gabriel Olanisakin; Babban Hafsan Sojin Kasa, Laftanar Janar Tukur Buratai; Babban Hafsan Sojin Ruwa, Vice Admiral Ibok Ekwe Ibas da Babban Hafsan Sojin Sama, Air Marshall Sadique Abubakar.

Akwai kuma Babban Sufeton ’Yan Sanda na Najeriya, Muhammad Adamu; Darakta Janar na Hukumar Leken Asiri, Ahmed Rufa’I Abubakar da Shugaban Hukumar Jami’an Tsaro na Farin Kaya, Yusuf Magaji Bichi.