Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya nada tsohon Sufeto-Janar na ’Yan Sanda, Solomon Arase, a matsayin sabon Shugaban Hukumar Harkokin ’Yan Sanda ta Najeriya (PSC).
Sai dai nadin nasa zai tabbata ne bayan Majalisar Dattawa ta amince da hakan.
- Majalisa ta bukaci CBN ya kara wa’adin daina karbar tsoffin kudi
- Babu gudu ba ja da baya kan wa’adin tsofaffin kudade – Emefiele
Wasikar da Buhari ya aike wa Majalisar wadda Shugabanta, Sanata Ahmad Lawan, ya karanto yayin zamansu na ranar Talata, ta nuna Buhari ya nada Arase ne ta yin madogara da sassa na 153 (1) da 154 (1) na Kundin Tsarin Mulki wanda aka yi wa gyara.
Idan nadin ya tabbata, Arase zai zama ya gaji Musiliu Smith a mukamin, wanda ya yi murabus a bara cikin yanayi mai rikitarwa
Kafin nadin nasa, shi ne shugaban sashen tattara bayanan sirri na Hukumar ’Yan Sandan Najeriya da Hukumar Leken Asiri da Binciken Manyan Laifuka.
Arase ya zama Sufeto-Janar na ’Yan Sanda a 2015 karkashin gwamnatin tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan bayan cire Suleiman Abba da ya yi a mukamin saboda rashin biyayya.