✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari ya kalubalanci malaman jami’o’i su nemo maganin COVID-19

Ya ce kamata ya yi jami’o’i su mayar da hankali wajen magance matsalolin al’umma.

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya kalubalanci malaman jami’o’in Najeriya da su yi kokari su gano maganin cutar COVID-19 don amfanin kasa.

Ya yi kiran ne yayin da yake jawabi a bikin yaye dalibai karo na 36 na Jami’ar Ilorin da ke Jihar Kwara a ranar Asabar.

Buhari ya kuma shawarci ’yan Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Kasa (ASUU) da su rungumi tattaunawa a matsayin hanyar magance matsaloli ba wai tsunduma yajin aiki ba.

Shugaban dai ya sami wakilcin Farfesa Ignatius Onimawo ne na Hukumar Kula da Jami’o’i ta Kasa (NUC).

Ya ce, “Kamata ya yi jami’o’i su mayar da hankulansu wajen yin bincike da magance matsalolin da suka addabi al’umma kamar cutar COVID-19, su nemo mafita don kasa ta samu ta ci gaba.

“A halin da muke ciki yanzu, bai kamata jami’o’inmu su sake shiga wani rikicin ba, la’akari da tsawon lokacin da aka bata saboda annobar Kwarona,” inji shi.

Ida za a iya tunawa, ko a kwanan nan sai da ASUU ta bayar da wa’adin gargadi tare da barazanar sake tsunduma yajin aiki saboda yadda suka ce gwamnati ta yi watsi da su.