✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Buhari ya isa Jos don kaddamar da yakin neman zaben Tinubu/Shettima

Ana sa ran Tinubu ya gabatar da manufofinsa yayin taron

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya isa Jos, babba birnin Jihar Filato, don halartar taron kaddamar da yakin neman zaben Shugabancin Kasa na jam’iyyarsa ta APC.

Za a kaddamar da yakin neman zaben Bola Ahmed Tinubu da Kashim Shettima ne a filin wasannin motsa jiki na Rawang Pam a jihar ranar Talata.

Bayanai sun nuna tun a ranar Litinin dan takarar Shugaban Kasa na APC, ya isa birnin na Jos don halartar taron.

Yayin taron, ana sa ran Tinubu ya gabatar da manufofi da tsare-tsarensa wanda Shugaba Buhari ya kaddamar kwannan nan a Fadar Shugaban Kasa da ke Abuja.

Ya zuwa lokacin hada wannan rahoton, an ga yadda aka girke jami’an tsaro a ciki da wajen taron.

%d bloggers like this: