✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari ya cancanci yabo kan kokarin murkushe Boko Haram – Wike

Gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Wike, ya yaba wa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari kan kokarin da ya ce yana yi ba kakkautawa wajen yaki da ’yan…

Gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Wike, ya yaba wa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari kan kokarin da ya ce yana yi ba kakkautawa wajen yaki da ’yan Boko Haram da ’yan bindigar da suka addabi Najeriya.

Gwamnan ya yi yabon ne a Gidan Gwamnatin Jihar da ke Fatakwal ranar Lahadi, jim kadan bayan jera furanni domin bikin ranar tunawa da ’yan mazan jiya ta bana.

Wike ya ce bayan barkewar Yakin Basasa, sojoji sun shafe shekara kusan 30 suna yaki wajen kwantar da tarzoma tare da tabbatar da cewa Najeriya ta ci gaba da zama kasa daya.

A cewarsa, tun daga lokacin, zai yi wahala a ce ga wata shekara da sojojin suka huta ba sa aikin kwantar da wata tarzoma a ciki ko a wajen Najeriya.

Gwamna Wike ya kuma ce sojojin na yaki da ’yan Boko Haram da sauran ’yan ta’adda a Jihohin Arewa maso Gabas da Arewa maso Yamma, da kuma ’yan bindiga a Jihohin Kudu maso Gabas.

Ya ce, “Ina yaba wa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari saboda aikin dawo da zaman lafiya a jihohin da ke fama da rikice-rikice.

“Kokarin wanzar da zaman lafiya a Najeriya da kuma shirya sahihin zabe su ne manyan abubuwan da za a ci gaba da tunawa da Buhari da su ko bayan ya sauka daga mulki.

“A matsayinmu na shugabanni, babban burinmu bai wuce na kokarin ganin Najeriya ta ci gaba da zama a matsayin dunkulalliyar kasa ba. Saboda haka, ba zan yi kasa agwiwa ba wajen yi wa Buhari da sauran shugabanni addu’ar ganin sun sauke wannan nauyin,” inji Gwamna Wike.