✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari ya ba Fashola biliyan N162 na gyaran hanyoyi

An fitar da biliyan 995.7 daga cikin kasafin kudin 2020 domin fara ayyuka

Gwamnatin Tarayya ta fitar da Naira biliyan 995.7 domin gudanar da ayyuka daban-daban na sabon kasafin kudin shekara 2020.

Ministar Kudi da Tsare-tsare Zainab Ahmed, ta bayyana haka a lokacin da ta mika wa Ministan Ayyuka, Babatunde Fashola Cekin Naira biliyan 162.667 da SUKUK ta samar.

“Shugaban Kasa Buhari, a lokacin sanya hannu kan sabon kasafin, ya bayar da umurni a sakin kashi rabin kudaden. Yanzu haka mun saki Naira biliyan N995. 665. In mun hada da na bashin SUKUK”, inji Ministar Kudin.

Zainab Ahmed ta ce gwamnati ta ware tiriliyan N1.347 domin aiwatar da ayyuka na zahiri a sabon kasafin na bana.

Ta ce, Naira biliyan 162.557 da aka damka wa Ma’aikatar Ayyukan, ciko ne na iya adadin kasafin kudin 2020 da gwamnati ta yi wa ma’aikatar, domin gudanar da ayyukanta daga bashin SUKUK.

A jawabinta, Darakta Janar ta Hukumar Kula Bashin Kasa, Misis Patience Oniha ta ce samun bashin kudin SUKUK ya samar wa gwamnati Naira biliyan 362.577 da za ta gudanar da ayyukan gyare-gyare da sabunta hanyoyi a yankunan siyasa shidda na Najeriya.

Bayan karbar cekin Naira Billiyan 162.6, Fashola ya nuna jin dadin karamcin da SUKUK ya yi wa Gwamnati Tarayya ya kuma ba da tabbacin aiwatar da ayyukan hanyoyi 44 da aka bayar da kudin domin su bisa inganci.