✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari ya ba da umarnin kafa sabbin Jami’o’i biyar

Nan ba da jimawa ba za a sanar da sunayen shugabannin jami'o'in.

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya amince tare da ba da umarnin kafa wasu sabbin jami’o’in Fasaha da na Harkokin Lafiya guda biyar don cike gibin da ake da shi na karancin likitoci, sashen bincike da kuma bangaren samar da magunguna.

Babban Sakatare a Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya, Arch Sonny Echono ne ya bayyana haka ranar Litinin a Abuja.

  1. Boko Haram: Bayan shekaru manoman Borno sun koma gona
  2. ECOWAS ta sanar da lokacin fara amfani da kudin bai-daya

Ya ce “Za a fara ginin sabbin Jami’o’in Fasaha biyu a bana, yayin da ragowar jami’o’in za a fara gininsu a shekara mai zuwa.

“Shugaba Buhari, ya kuma amince a fidda Naira biliyan hudu ga kowace daya daga cikin jami’o’in fasahar biyu da za a samar, da kuma biliyan biyar ga kowace daga cikin Jami’o’in Harkokin kiwon lafiya.

“Za a fitar da wadannan kudade ne daga asusun Hukumar Bunkasa Jami’o’i ta Kasa (TETFund).”

Echono, ya bayyana cewa za a samar da jami’o’in Fasahar biyu a jihohin Jigawa da Akwa Ibom, yayin da kuma za a kafa na harkokin kiwon lafiyar a garin Azare na Jihar Bauchi da kuma Ila Orangun, a Jihar Osun.

Babban sakataren, ya tsegunta wa manema labarai cewa tuni Shugaba Buhari ya zabi Shugabannin Jami’o’in da zai nada, wanda za a sanar da sunayensu nan ba da jimawa ba.