✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Bom ya kashe dan ta’adda garin kai wa jami’an tsaro hari

Wani dan ta'adda ya mutu sakamakon tashin rigar kunar bakin wake da yake sanye da ita da nufin kai wa jami'an tsaro hari a Jihar…

Wani dan ta’adda ya mutu sakamakon tashin rigar kunar bakin wake da yake sanye da ita da nufin kai wa jami’an tsaro hari a Jihar Kaduna.

Dan ta’addan ya gamu da ajalinsa ne a yayin da jami’an tsaro ke tsananta kai samame maboyar ’yan ta’adda a jihohin Kano da Kaduna.

A samamem da sojoji da jami’an hukumar tsaro ta DSS da ’yan sanda suka kai a jihohin, sun kwato bindigogi biyu da rigunan kunar bakin wake guda biyu da gurneti biyu da kwamfuta da kuma wayoyin hannu guda 11.

Kakakin hukumar DSS, Peter Afunanya, ya ce mutun biyu su shiga hannun jami’an tsaro a yayin samamen.

Afunanya ya ce an kai samame ne bayan samun rahoto cewa wasu gawurtattun ’yan ta’adda na kokarin taruwa a Yankin Arewa maso Yammacin Najeriya da nufin tayar da fitina bayan sojoji sun tarwatsa su a Arewa maso Gabas.

Ya kara da cewa hukumomin tsaro ba za su yi wata-wata ba wajen ragargaza duk masu neman tayar da fitina musamman a lokacin da ake kokarin rantsar da sabuwar gwamnati.