✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Bollywood: Aamir Khan ya saki matarsa

Jarumin ya rabu da matarsa bayan shafe shekaru 15 suna tare.

Fitaccen jarumin masana’antar nan ta Bollywood mai shirya fina-finai a Indiya, Aamir Khan, ya saki matarsa, Kiran Rao bayan shafe shekara 15 suna tare.

Khan da Rao sun bayyana rabuwar tasu cikin wata sanarwa da suka fitar, sai dai sun ce za su ci gaba da kula da yaransu tare.

  1. An kayyade farashin takin zamani kan N5,000
  2. Ba zan taba bari Iran ta mallaki makamin Nukiliya ba – Biden

Sanarwar ta ce, “A cikin wadannan shekaru 15 masu dadi da muka yi tare mun yi rayuwa cikin farin ciki da jin dadi, kuma soyayyarmu ta bunkasa ne kawai cikin aminci, girmamawa da kauna.

“Amma yanzu muna son mu bude sabon shafi a rayuwarmu, ba a matsayin mata da miji ba, sai dai a matsayin iyaye da kuma ‘yan uwan juna,” a cewar sanarwar.

Ma’auratan sun hadu a shekarar 2001 yayin shirin wani fim wanda Kiran Rao ta yi aiki a matsayin mataimakiyar mai bada umarni.

Bayan shafe shekaru suna soyayya, sai suka yi aure a shekarar 2005 kuma Mai Duka ya azurta su da yara uku.