✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Boko Haram ta kashe mayakanta 300 da suka yi niyyar mika wuya a Sambisa

Mayakan dai na shirin mika wuya ne lokacin da aka kashe su

Wasu kwamandojin Boko Haram/ISWAP da ba su tuba ba sun kashe dakarunsu sama da 300 da iyalansu da ke fitowa daga dajin Sambisa da nufin mika wuya  a Jihar Borno.

Kwamandojin dai sun katse hanzarin mayakan ne da nufin kawo cikas kan kokarin tattaunawar da suke yi da gwamnatin jihar.

Mai ba gwamnan Jihar Borno shawara kan harkokin tsaro, Birgediya Janar Ishaq Abdullahi (mai ritaya), ne ya bayyana haka a wata hira da manema labarai a Maiduguri ranar Alhamis.

A cewarsa, sama da mayakan Boko Haram 90,000 da iyalansu ne ya zuwa yanzu suka mika wuya ga gwamnatin jihar Borno a cikin watanni 17 da suka gabata tun bayan fara tattaunawar zaman lafiya da ake yi da su.

Ya yi nuni da cewa, kaso 95 cikin 100 na kwamandojin Boko Haram ne ake kashewa ko dai ta hanyar ayyukan soji ko kuma ta hanyar fada tsakanin bangarorin da ke gaba da juna.

Birgediya Janar Ishaq ya ce, “Amfanin da muke da shi a wannan tattaunawa ta zaman lafiya shi ne rasuwar marigayi Abubakar Shekau da kuma yadda jama’a ke da kudurin yin hakuri su zauna tare da wadannan ’yan ta’addan wuri guda.

“Sun yi gargadin cewa babu wanda ya isa ya amsa kiran wajen tattaunawar matukar sun san da haka take za su kashe wadda duk suka samu da hakan, a zahiri kan hakan sun kashe mayakansu sama da 300 da iyalansu da ke fitowa daga dajin na Sambisa,” in ji shi.

A cewarsa, ko a makon da ya gabata sai da ’yan kungiyar suka kashe wasu kwamandoji uku da iyalansu da ke shirin tserewa don mika wuya, inda ya ce hakan ya jima yana faruwa.

“Don haka duk wani dan Boko Haram da ya mika wuya da ka gani a sansanin a yanzu to kasada da ransa ya yi ya fito. Abin takaici ne yadda kwamandojin ke kashe yara, mata da nakasassu da suka fahimta na shirin tserewa ne daga cikinsu.

“Har wayau a makon da ya gabata ma aka samu wani bidiyo da suka sanya jajayen kaya a jikinsu, wadda Amir ne ya amince da fitar su amma abin takaici an halaka su don sanya tsoro ga wadanda suke son mika wuya,”  in ji Birgediya Janar Ishaq.

Sai dai ya alakanta irin nasarar da ake samu a kan ’yan ta’addan da addu’o’in da al’ummar Borno suka yi da kuma manufofin siyasa na gwamnati mai ci aJjihar.