✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Boko Haram ta banka wa gari wuta a Borno

Akalla fararen hula biyar ne kungiyar Boko Haram ta kashe a hare-haren da ta kai a jihar Borno. Mayakan kungiyar sun banka wa kauyuka wuta…

Akalla fararen hula biyar ne kungiyar Boko Haram ta kashe a hare-haren da ta kai a jihar Borno.

Mayakan kungiyar sun banka wa kauyuka wuta da tsakar dare bayan sun ci karfin mazauna a karamar hukumar Konduga.

Da daren Lahadi ne maharan suka far wa kauyen Kondori inda suka kashe mutum hudu suka kuma sa wa kauyen wuta.

“Yanzu haka babu kowa ya tsere saboda sun kona kauyen kurmus.

“A take suka harbe mutum uku suka jikkata wasu hudu. Mutum na hudun shi ma ya rasu,” inji ‘yan sintirin yankin.

A wani hari da mayakan suka kai karamar hukumar Jere, sun banka wa sakatariya wuta suka kuma kwashi wasu kayan yaki.