✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Boko Haram: Nakiyoyi sun kashe fararen hula 755 a Najeriya

Fargabar tana hana musu shiga cikin dazuka ballantana su noma gonakinsu

Hukumar Kawar da Ababen Fashewa ta Majalisar Dinkin Duniya (UNMAS) da hadin gwiwar cibiyar samar da zaman lafiya da tallafi da kawayensu sun ce fararen hula 755 ne nakiyoyi suka kashe a Najeriya cikin shekaru shida da suka gabata.

Hukumomin sun bayyana cewa wasu karin fararen hula 1,321 sun jikkata a sakamakon fashewar nakiyoyi a tsawon lokacin, don haka suka yi kira ga gwamnatin Najeriya ta kafa cibiyar kula da kawar da nakiyoyin da ba su fashe ba.

Kodineta na Kasa kan shirin kawar da nakiyoyi, Guruf Kyaftin Sadeeq Garba Shehu (murabus) ne ya sanar da haka a taron ranar wayar da kan jama’a kan illolin nakiyoyi da aka gudanar a Maiduguri.

Ya ce ko da yake an ci karfin matsalar tsaro a yankin Arewa maso Gabashin Najariya, har yanzu rayukan al’ummomin da ke komawa garuruwansu a yankin na fuskantar barazana saboda yaduwar abubuwan fashewa, lamarin da ke hana su ’yancinsu na walwala.

Bugu da kari, fargabar tana hana musu shiga cikin dazuka ballantana su noma gonakinsu, wanda hakan yake barazana ga samar da wadataccen abinci.

Ya kara da cewa, “a shekaru uku da suka gabata, Najeriya ce kasa ta biyu a duniya wajen yawan mutanen da aka kashe da hanyar kunar bakin wake, inda ’yan kunar bakin wake suka kashe mutum 619.

“Har yanzu akwai wuraren da abubuwan fashewa da aka jefa ba su fashe ba, wanda ke bukatar sai an share wuraren domin manoma su samu tabbaci da kwanciyar hankalin noma gonakinsu.”

Da yake jawabinsa, Daraktan Jinkai a Ma’ikatar Agaji da Ayyukan Jinkai ta Tarayya, Grema Alhaji Kadi, wanda ya wakilci ministar ma’aikatar, Sadiya Umar Farouq, ya bayyana cewa Gwamnatin Tarayya ta mayar da hankalinta wajen tabbatar da ganin a kawar da iri wadannan abubuwan fashewa daga yankunan da ke fuskantar barazanar.

Ya kuma yaba wa hukumomin kasashen duniya bisa irin taimakon da suke ba wa Najeriya wajen gane hakan ya samu.