✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Birtaniya ta gargadi ’yan kasarta kan zuwa wasu jihohi 12 a Najeriya

Akwai yiwuwar sace ma’aikata ’yan kasashen waje.

Gwamnatin Birtaniya ta gargadi ’yan kasar da su guji zuwa jihohi 12 a Najeriya, inda ta ce akwai yiwuwar kungiyar Boko Haram ta yi garkuwa da ’yan kasashen waje.

Ofishin jakadancin Burtaniya da ke Abuja ya ce akwai bayanan da ya samu cewa ana shirin kaddamar da satar ’yan kasashen waje da sunan neman kudin fansa ko kuma siyasa.

Jihohin sun hada da Borno da Yobe da Adamawa da Gombe da Kaduna da Katsina da Zamfara da Delta da Bayelsa da Ribas da Akwa Ibom da kuma Kuros Riba.

Ofishin ya kuma kara da cewa, an farmaki ma’aikatan jin-kai a wasu hare-hare da aka kaddamar a Arewa maso gabashin Najeriya, da suka hada da na garin Monguno a ranar 13 ga watan Yunin 2020.

Wani bangaren sanarwar ya kuma ce “yanayin tsaro ya kara tabarbarewa a Arewa maso Gabashin Najeriya tun 2018.

“Saboda haka akwai yiwuwar sace ma’aikata ’yan kasashen waje,” a cewar sanarwar.