✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Biloniya mai kamfanin Crypto ya tsiyace cikin watanni

Ana zarginsa da karkatar da biliyoyin dalolin masu zuba hannun jari.

Mista Sam BankmanFried Babban Jami’in Gudanarwa ne a daya daga cikin manyan kamfanonin hada-hadar kudaden intanet na Crypto, wato FTX, wanda a halin yanzu ya shiga cikin rudani bayan dukiyarsa ta fadi warwas, inda a yanzu ya mallaki kasa da Dala dubu 100 kacal.

Tsohon hamshakin attajirin ya mallaki dukiyar da ta kai Dala biliyan 24, a watan Maris din bara, (kimanin Naira tiriliyan 17), wato yana sama da attajirin Afirka Aliko Dangote, inda ya fara fuskantar tuhume-tuhume a bara da farkon bana, lamarin da ya sa shi tunanin yadda zai dauki nauyin lauyoyin da za su kare shi.

Mista Bankman-Fried ya ki amsa tuhume-tuhumen da ake yi masa da suka hada da damfarar masu zuba hannun jari biliyoyin kudade, inda a yanzu yake jiran shari’ar da aka shirya za a fara nan da wata tara.

Tsiyacewarsa Mista Bankman na daya daga cikin hamshakan attajirai masu hada-hadar kudin crypto kafin kasuwancinsa ya shiga muwuyacin hali.

Ya shiga halin ni-’yasu bayan kasancewar hamshakin biloniya a hada-hadar kudin Kirifto, lokacin da kamfanoninsa na FTX da Alameda Resarch suka durkushe a watan Nuwamban bara.

Dan kasuwar na Wall Street Sam Bankman-Fried da tsohon ma’aikacin Google, Gary Wang ne suka kafa Kamfanin FTX a 2019.

Matsalar ta faro ne a Nuwamban bara, lokacin da shafin watsa labara na kudin crypto wato CoinDesk ya ba da rahoton cewa, gaba dayan dukiyar Bankman ta dogara ne a kan Kamfanin Alameda Research da kuma hannun jarinsa na FTT.

Baya ga haka, sayar da duk wani hannun jari da ya mallaka a Kamfanin FTT da Shugaban Kamfanin Binance, Mista Changpeng Zhao ya yi saboda wasu bayanai da ba a bayyana ba, a cewar Reuters ya kara taimakawa wajen dukushewarsa.

Yunkurin da Kamfanin Binance ya yi ya tayar wa masu hannun jari hankali, inda cikin gaggawa suka janye dukkan kudadensu a lokaci guda.

Don haka wannan lamari ya jawo wa asusun ajiyar kudade na FTX ya koma fanko, inda darajar hannun jarin FTT ta ragu.

Mista Sam Bankman-Fried ya fara fuskantar karayar arziki, inda dukiyarsa ta yi kasa daga Dala biliyan 16 (Naira tiriliyan 11) zuwa kasa da Dala miliyan 991 (Naira biliyan 708) a rana guda.

Karayar arzikin nasa ya ci gaba har zuwa watan Disamban bara, lamarin da ya tilasta aka sa shi a sahun matsiyata.

A farkon bana dukiyar Mista Sam Bankman-Fried ba ta kai Dala 100 ba (wato Naira miliyan 72), inda a yanzu yake zaune tare da iyayensa.

Zargin da ake yi masa a yanzu ya sa an tisa keyarsa daga Bahamas zuwa Amurka don fuskantar tuhumar zamba da almundahana.

Ana zarginsa da karkatar da biliyoyin dalolin masu zuba hannun jari don sayen gidaje da ba da gudummawar siyasa da kuma bunkasa kamfaninsa na hada-hadar kudin Crypto, wato Alameda Research.

Idan har aka same shi da laifi zai iya fuskantar hukuncin daurin shekara 115.

Hamshakin attajirin wanda ya fara kafa kamfanin hada-hadar kudin Crypto ya yi asarar kudi da ya kai kimanin Dala biliyan 116 daga watan Maris din 2022.

Babban wanda ya yi asara shi ne wanda ya kafa Kamfanin hada-hadar kudade na Binance, Mista Changpeng Zhao, wanda dukiyarsa ta yi kasa sosai daga Dala biliyan 65 (wato Naira tiriliyan 46) a farkon watan Maris na bara zuwa Dala biliyan 4.5 (wato Naira tiriliyan 3.217) a halin yanzu.