✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Bikin Sallah: Tsakanin Fulani da Ja-gadi a Nasarawa

Fulani kan halarci wasan daga wurare daban-daban kamar Yola, Bauchi, Kano, Kaduna, Lokoja da sauransu.

Ja-gadi wasan Sallah ne da Fulani suka saba gudanarwa duk shekara a garin Keffi da ke Jihar Nasarawa a yankin Arewa maso Tsakiyar Najeriya.

A duk jajibirin Sallah karama ko babba, Fulani musamman matasa (maza da mata) daga sassa daban-daban sukan yi tururuwa zuwa Keffi inda suke haduwa su yi wasa don sada zumunta, debe kewa da kuma nishadi.

Ja-gadi dadaddiyar al’adar Fulani ce a garin Keffi wadda ta kasance fage na samun nishadi da shakatawa, sada zumunta da sauransu ga wadanda lamarin ya shaf.

Wasu lokuta, wansan kan zama sila na samun mata ko mijin aure ga wasu mahalarta.

Malam Abdullahi Usman shi ne Madakin Masarautar Keffi, ya shaida ma wakilinmu cewa, “Wasan Sallah (Ja-gadi) da Fulani suke zuwa a garin Keffi dadaddiyar al’ada ce, kasancewar Keffi gari ne na Fulani.

Fulani kan halarci wasan daga wurare daban-daban, kusa da nesa, kamar Yola, Bauchi, Kano, Kaduna, Lokoja da sauransu.

“A shekarun baya, idan suka shigo sai sun shafe kwana bakwai suna wasa kafin kowa ya koma inda ya fito.

“Da tafiya ta yi tafiya, komai ya sauya, shi ya sa Masarautar Keffi ba ta bari suna dadewa a gari saboda dalilai na tsaro,” in ji Usman.

Lokacin da aka fara Ja-gadi a Keffi

Game da lokacin da aka fara gudanar da Ja-gadi a garin Keffi Malam Usman ya ce, “soma gudanar da wannan wasa ya kai shekaru 200, saboda tun kafuwar garin Keffi aka fara gudanar da shi.

“Kuma sun zabi zuwa Keffi ne saboda asali gari ne na Fulani, suna jin dadin garin bisa ga sauran wurare.”

Malamin ya kara da cewa, akasin da ake samu wani lokaci, shi ya sa ake hana Fulani shigowa gari kamar yadda suka saba.

ja-gadi
Wani sashen mahalarta Ja-gadi

“Kalubalen da wani lokaci muke fuskanta dangane da shigowar Fulani wasan Sallah a Keffi shi ne, sukan yi rikici yasu-yasu wanda wani lokaci yakan haifar da asarar rai da yi wa juna rauni.

“Shi ya sa ma wani lokaci ake hana su shigowa baki daya idan aka hararo cewa za a iya samun matsala da shigowar tasu.”

Amfanin Ja-gadi ga jama’ar gari

Ko shakka babu, Ja-gadi na tattare da wasu alfanu wadanda jama’ar gari kan amfana da su a duk lokacin da Fulani suka shigo, kamar dai yadda Madakin Keffi ya bayyana.

“Jama’ar gari na amfana da zuwan Fulanin, saboda duk lokacin da suka shigo gari masu sana’a kan samu ciniki sosai. Misali, kamar masu sayar da abinci, masu harkar daukar hoto da sauransu.

“Haka nan, wasan kan zama wata hanya ta raya kyawawan al’dun Fulani, kamar sharo, yanayin suturar Fulani, sada zumunta da sauransu. Kuma fage ne na yawon shakatawa da samun nishadi,” in ji Malam Usman

Takaitaccen Tarihin Keffi

Keffi gari ne mai dadadden tarihi wanda ya kafu sama da shekaru 200 da suka shude kamar dai yadda masanin tarihin garin, Malam Muhammad Gali Umar (Wamban Taka Lafiyan Zazzau) ya sanar da wakilinmu.

“Da farko dai an kafa garin Keffi ne a shekarar 1798, kuma asalin wanda ya kafa garin Bafulatani ne, wato Malam Abdullahi Zanga, wanda ya fito daga ‘Yan Tumaki a Jihar Katsina. Shi ne ya yi sarki na farko a garin inda Allah Ya yi masa rasuwa a 1820, shekara 22 ya yi a kan gadon sarauta.”

Malamin ya ce, yadda Fulani kan yi Ja-gadi a baya abin da gwanin ban-sha’awa da burgewa sabanin yadda lamarin yake a yau.

Ya ce, “Sukan shigo gari mazansu da matansu a yi wasa da dariya da sharo da sauransu. Amma a wannan zamani labari ya canja, saboda ana samun bata-gari a cikinsu da kan haifar da matsala, a wasu lokutan sai an hada da jami’an tsaro kafin a samu sa’ida.

“Akwai masu zuwa daga nesa, kamar Nijar, Borno, Mali, Kamaru, Senigal, Gambia da sauransu,” in ji Umar.

Binciken wakilinmu ya gano cewa, wasu mahalarta wasan iyayensu ne kan dauki nauyin tafiyarsu inda sukan kama dabba su sayar don yi wa yaran kudin guziri.

Alama ce ta jarumta

Idris wanda aka fi sani da Sharon, na daya daga cikin mahalarta Ja-gadi na wannan lokaci daga garin Nasarawa, ya fada wa Aminiya cewa a fahimtarsa, halartar Ja-gadi na nuna jarumtar matashi, saboda ba wurin zuwan matsorata ba ne.

Idris (Sharon)

“Halartar Ja-gadi jarumta ce saboda matsoraci ba zai iya zuwa a yi da shi ba. Ina jin dadi sosai da halartar Ja-gadi don kuwa, hakan na ba ni damar haduwa da ’yan’uwa daga wurare daban-daban, kamar ’yan Zamfara, Ilori, Enugu da sauransu.”

Baude wa gargajiya

Wani al’amari mai daukar hankali game da Ja-gadi shi ne, yanayin shigar da mahalartan kan yi, inda galibinsu suke amfani da suturar da ba a san gargajiyar Fulani da su ba.

A cewar Audu Usman, “Kafin wannan lokaci, mahalarta Ja-gadi kan zo ne cikin sutura da suka kebanta da gargajiyar Fulani, amma a yau lamarin ya sauya saboda tasirin zamani.

“A yau, galibinsu sun rungumi al’adar aro ta yin mu’amala da kananan kaya irin su shet-shet, wandunan jins da makamantansu, sai kuma batun askin zamani da rina suma da launi daban-daban da dai sauransu.”

Ko yaya jama’ar gari kan yi fama da batun bai wa wadannan bakin nasu masauki a duk lokacin da suka shigo gari?

Tambayar da Gali Umar ya amsa mana kenan da cewa: ”Jama’ar gari kan ba su wurin kwana ba tare da wata tsangwama ba. Wasu har cikin gida ake shigar da su a ba su wurin kwanciya, wasu a zaure, wasunsu kuwa a filin Allah suke kwana.”

A karshe, bisa la’akari da yadda Ja-gadi kan gudana, zai yi matukar kyau da armashi idan Masarautar Keffi ta shigo ta hada kai da Karamar Hukumar Keffi da ma Gwamnatin Jihar Nasarawa, wajen fitar da wani tsari da zai taimaka wajen tsaftace yadda ake Ja-gadi tare da inganta shi ta yadda zai kwadaita da kuma jawo hanakali jama’a na kusa da nesa wadanda ba Fulani ba, hakan ka iya zama wata hanya ta samun kudin shiga ga Masarautar Keffi, Karamar Hukumar Keffi da ma Jihar Nasarawa baki daya.