✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Bikin Ranar Dimokuradiyya: Sojoji 3 sun suma ana tsaka da fareti a Abuja

Ana zargin dadewa a rana ce ta jawo musu faduwar

Wasu jami’an sojoji uku sun suma yayin da ake tsaka da faretin Ranar Dimokuradiyya ta bana a filin Eagle Square da ke Abuja.

Rahotanni sun ce ana zargin tsayuwa cikin rana na tsawon lokaci da kuma gajiya ne suka sanya sojojin suka zube a wajen.

Faduwarsu ke da wuya jami’an tsaro da ma’aikatan lafiya suka yi musu kawanya, inda aka dauke su zuwa wajen da aka ba su agajin gaggawa.

Daga bisani dai an ba su agajin da ya kamata inda suka dawo cikin hayyacinsu.

A hannu guda kuma, Rundunar Tsaro ta Sojoji Mata ma sun gudanar da nasu faretin, da kuma rawar al’ada daga al’ummar Najeriya daban-daban.

Shugaban Kasa Buhari dai shi ne babban bako na musamman a wajen bikin da aka gudanar ranar Litinin, kuma sojoji sun take masa baya da salon tafiya a hankali da kuma sauri-sauri a lokuta mabambanta.