✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Benzema ya kwaci Real Madrid a hannun Sevilla

Real Madrid ta farko kwallaye biyu ta kara wa Sevilla a gasar La Liga

Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid  ta kwaci kanta da kyar a hannun Sevilla a gasar La Liga a karawarsu ta daren ranar Lahadi.

Babban dan wasan Real Madrid, Karim Benzema, ne ya kwace ta bayan an kusa tashi wasan a kunnen doki, a wasan da Sevilla ta fara zura wa kungiyar kwallo biyu da nema.

Barayi sun fasa gidan Benzema lokacin da Madrid ke wasa

Real Madrid ta tallafa wa yaran da yakin Ukraine ya mayar ’yan gudun hijira

A farkon wasan, Sevilla ta rike wa Real Madrid wuta, har zuwa zagaye na biyu tana kan gaba.

Ana ganin rashin katabus din Real Madrid a farkon wasan  na da nasaba da tasirin dukan da ta sha a Gasar Zakarun Turai a baya-bayan nan.

Sai dai kuma da aka dawo zagaye na biyun wasan, Real Madrid ta gyagije ta dagula wa Sevilla lissafi, inda ta farke kwallayen biyu. daga nan kuma suka ci gaba gumurzu, a yayin da lokacin tashi yake kara karatowa.

Bayan an yi ta fafatawa a haka ne, ana dab da tashi wasan gaban Real Madris, Karim Benzema, ya zura kwallo na uku a ragar Sevilla, a haka aka tashi wasan, tana da ci 3, Sevilla kuma 2.