✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Bene mai hawa 7 da ake aikin gina shi ya rushe a Legas

Sai dai ana tunanin babu kowa a cikinsa lokacin da ya rushe

Wani bene mai hawa bakwai da ake aikin gina shi ya rushe a unguwar masu ido da kwalli ta Banana Island da ke Ikoyin Jihar Legas.

Lamarin ya faru ne wajen misalin karfe 3:00 na ranar Laraba.

Jaridar Punch ta rawaito cewa rushewar ta faru ne lokacin da wasu daga cikin masu aikin ginin suka riga suka tashi daga aiki.

Kakakin Hukumar Kashe Gobara ta Jihar, Amodu Shakiri, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Ya ce, “An kira mu wajen misalin karfe 3:000 na yamma. Yanzu haka muna kokarin tabbatar da cewa babu kowa a cikin ginin lokacin da ya rushe.”

Jihar Legas dai ta yi kaurin suna wajen yawan rushewar dogayen gidaje a Jihar. Ko a watan Nuwamban 2021 sai da sama da mutum 50, ciki har da mamallakin wani gida suka mutu bayan ya rushe ana tsaka da aikin gina shi.

Tuni dai gwam,natin Jihar ta yi wata dokar da za ta ba ta damar kwace lasisin filin duk wani ginin da ya rushe a matsayin wata hanyar yi wa tufkar hanci.