✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Bello Turji ya sako mutum 52 da ya yi garkuwa da su a Zamfara

Mutanen da aka sako suna kan hanyar zuwa garin Shinkafi.

A yau Litinin ce rahotanni suka bayyana cewa Bello Turji, daya daga cikin gagararrun ’yan bindigar da suka addabi Jihar Zamfara da kewaye, ya sako wasu mutum 52 da suka shafe lokaci mai tsawo a tsare a hannunsa yana garkuwa da su.

Majiyar rahoton da ta nemi a sakaya sunanta, ta shaida wa wakilinmu cewa, a halin yanzu mutanen da suka shaki iskar yanci suna kan hanyarsu ta fitowa daga jeji inda ake tsare da su zuwa wani wuri wanda daga nan za a garzaya da su garin Shinkafi.

“An debi mutanen a cikin wasu motoci kirar bus wanda a halin yanzu suna kan hanyar zuwa Maberiya, wani yanki mai tazarar kilomita 5 da kudancin garin Shinkafi,“ a cewar majiyar.

Bayanai sun ce Turji shi ne ja gaba a kashe-kashe da sace-sacen mutane da ake yi domin neman kudin fansa a yankunan Kananan Hukumomin Shinkafi, Sabon Birni da kuma Karamar Hukumar Isah a Jihar Zamfara da Sakkwato.

A watan jiya ne Turji ya bayyana aniyyar cewa zai zubar da makamai ya rungumi zaman lafiya a cikin wata wasikar neman sulu da ya aike wa Masarautar Shinkafi.

Majiyoyi sun ce tattaunawar da ake yi da Turjin ce a halin yanzu ta kai ga sako wadannan mutane da suka shafe tsawon lokaci yana garkuwa da su.