✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Ya tozarta dan jaridarta kuma yana neman ta biya shi biliyan shida’

Tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama na Najeriya, Femi Fani-Kayode ya yi kurarin maka kamfanin Media Trust a kotu in ba ta biya shi diyyar Naira…

Tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama na Najeriya, Femi Fani-Kayode ya yi kurarin maka kamfanin Media Trust a kotu in ba ta biya shi diyyar Naira biliyan shida ba.

Fani-Kayode ya yi barazanar ce a cikin wasikar da ya yada a wasu kafofin, amma bai kai wa kamfanin ba, kwana biyu bayan ya nemi gafara kan cin mutuncin da barazana ga lafiyar da ya yi wa wakilin jaridarta na Daily Trust da Aminiya a garin Kalaba.

Bidiyon yadda Fani-Kayode ya yi wa dan jarida Eyo Charles ta jawo masa la’anta daga fadin duniya tare da kiran sa da ya janye kalaman da barazanar da ya yi wa Mista Eyo Charles.

Tambayar da Charles ya yi wa tsohon ministan wanda ke zagayayen duba ayyukan gwamnoni — alhalhi shi ba jami’in gwamnati ba ne — ta bukaci sanin manufar yin hakan da kuma wanda ke daukar nauyin tafiye-tafiyen.

Fani-Kayode ya dauki lokaci yana zagin Charles da yi barazanar taba lafiyarsa, har sai da aka sa baki, duk da cewa dan jaridar bai ce masa uffan ba.

‘Yan jarida da sauran masu sharhi sun yi amfani da kafofi iri-iri domin mayar masa da martani tare da caccakar abin da tsohon ministan ya yi.

Akalla sau biyu tsohon Fani-Kayode na bayyana nadama game da abin da yi wa Charles a matsayin abin kunya da ya ja wa kansa da iyalansa tare da zubar da kimar kansa a idon masu ganin sa da mutunci.

Daga baya ya fito da sanarwar cewa wani ra’ayi da ke martani ga abin da ya yi wa Charles da aka wallafa a jaridar Daily Trust cin mutumci ne da zubar masa da kima a idon duniya.

Lauyoyinsa sun ce yana bukatar Media Trust ta biya shi ‘Naira biliyan shida da bai taka kara ya karya ba’, sannan ta janye ra’ayin da ya soke shi.

Yana kuma butata ta wallafa janye sharhin a wasu manyan jaridu biyu, sannan ta fara sasantawa da shi.

Ya ce muddin jaridar ba ta yi haka ba cikin sati biyu, to ta kwana da shirin haduwa da shi a kotu.