✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Batanci: ’Yan sanda sun gana da malaman addini a Gombe

Kwamishinan ’yan sandan Gombe ya bukaci hadin kan shugabannin addinai biyu don kaucewa rikici.

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Gombe, ta yi zaman gaggawa da malaman addinin Musulunci da na Kirista don neman a zauna lafiya a yayin da ake zaman dar-dar a Jihar Sakkwato bisa kisan dalibar Kwalejin Ilimi na Shehu Shagari, kan zagin batanci ga Annabi Muhammad (SAW).

Zaman da ya gudana a hedikwatar ‘yan sandan jihar, ya samu wakilcin malaman addinin Musulunci da na Kirista a fadin jihar.

Yayin zaman, Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Gombe, Ishola Babatunde Baba’ita, ya karfafa batun zaman lafiya da fahimtar juna a tsakanin mabiya addinan biyu a duk fadin jihar.

Ya jinjina wa malaman addinan kan yadda suke wa’azantar da mabiyansu, sannan ya hore su da su hada kai da ’yan sanda wajen tabbatar da bin doka da oda

Wakilai daga Kungiyar Jama’atu Nasril Islam (JNI) da Kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN) sun ba da tabbacin cewa da za su zauna lafiya da juna tare da fadakar da mabiyansu muhimmancin zaman lafiya.

Da yake jawabi a wajen taron, Alhaji Sale Danburam, Sakatare-Janar na JNI, cewa ya yi zaman lafiya shi ne kashin bayan kowanne addini, inda ya ce ko addini ba za a gudanar ba muddin babu zaman lafiya.

Danburam, ya jinjina wa kwamishinan bisa yunkurin da ya yi na samar wa jihar zaman lafiya.

Shi ma Shugaban Kungiyar CAN Reshen Jihar Gombe, Rabaran Joseph Shinga, cewa ya yi zaman lafiya abu ne da ya shafi kasa, don haka ya yi wa kwamishinan alkawarin ci gaba da zaman lafiya da juna.

Ya ce Gombe an yi ittifakin ita ce Jihar da aka fi sauran jihohi zaman lafiya a Najeriya.

Mahalarta taron sun tofa albarkacin bakinsu na bayyana muhimmancin zaman lafiya a tsakanin al’umma, kuma suka yi alkawarin cewa za su goyi bayan ci gaba da zaman lafiyar.