✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Batanci: An sanya dokar hana fita a Sakkwato

Zanga-zangar lumana ta rikide zuwa tarzoma a yankunan Sakkwato ranar Asabar.

Gwamnatin Jihar Sakkwato ta sanya dokar hana fita gaba daya bayan barkewar rikicin da ya biyo bayan kisan wata daliba da ake zargi da batanci ga Manzon Allah (SAW).

Tambuwal ya sanya da dokar hana fita ta awa 24 a Jihar Sakkwato ne domin dawo da zaman lafiya a birni da kewayen jihar.

A safiyar Asabar ne aka tashi da zanga-zangar lumana domin neman a sako mutanen da aka kama da zargin sun kashe Daborah Yakubu kan ta yi batanci ga Manzon Allah (SAW).

Zanga-zangar lumana ta juya zuwa tashin hankali a wasu unguwanni abin da ya kai ga sanya dokar nan take.

Tun a ranar Juma’a Gwamnan Tambuwal ya yi zama da malaman Musulunci da jami’an tsaro a kokarin hana barkewar rikici kan batun batancin.