✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Batanci ga Annabi: Kotu ta warware hukuncin kisa da aka yanke wa Matashi a Kano

Kotun ta warware hukuncin kisa da aka yanke wa Aminu Yahaya Sharif.

Kotun Daukaka Kara da ke zamanta a Jihar Kano, ta warware hukuncin kisa da aka yanke wa Aminu Yahaya Sharif, wani mawakin da aka samu da laifin batanci ga fiyeyyen halitta, Annabi Muhammad (SAW).

Kotun ta yanke hakan ne a ranar Alhamis, 21 ga watan Janairun 2021, inda ta riki dalilin cewa hukuncin da wata kotun shari’ar Musulunci a Jihar Kano ta yanke wa matashi cike yake da kura-kurai.

Kazalika, kotun ta warware hukuncin cin sarka na tsawon shekaru goma da aka yanke wa  Umar Faruk, wani yaro dan shekara 13 da aka kama da laifin batanci.

Aminiya ta ruwaito cewa, wata Kotun Shari’ar Musulunci ta Jihar ce ta yanke wa Aminu Yahaya Sharif hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan ta same shi da laifin yi wa Manzon Allah (SAW) batanci a wani sakon sauti da ya yi ta manhajar WhatsApp tun a watan Fabrairun 2020.

A zaman kotun na baya, lauyan masu daukaka karar, Barista Kola Alapinni ya bukaci Babbar Kotun ta yi watsi da hukuncin Kotun Musuluncin, bisa hujjar cewa ba a yi wa wadanda yake karewa adalci ba, kuma shari’ar ta saba da tsarin dokar kasa.

A nata bangaren, lauyar Gwamnatin Jihar Kano, Barista Aisha Mahmud ta yi kira ga Babbar Kotun da ta tabbatar da hukuncin Kotun Musuluncin ta yi watsi da bukatar masu daukaka karar.

Daga baya ne Mai Shari’a Nasiru Saminu ya sanar da ci gaba da shari’ar a ranar Alhamis 21 ga Janairu, 2021, sai dai kuma an dan samu jinkiri lokacin saboda ranar rasuwar da aka yi masa.